Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
Published: 29th, July 2025 GMT
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin.
Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen.
Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa.
Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama.
Dr Shuaibu ya bayyana cewa, sauran mutane 9 da ke cikin jirgin har yanzu ba a same su ba a lokacin da ake bayar da wannan rahoto.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, ba a fitar da sunayen waɗanda abin ya shafa ba, amma lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da baƙin ciki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa, za a raba rigunan kariya (life jacket) ga fasinjoji a nan gaba kadan domin kiyaye sake afkuwar lamarin nan gaba.
Ya kuma gargadi matuka kwale-kwale da su kiyaye ƙa’idojin tsaro da kaucewa cunkoson fasinjoji, musamman da yamma a lokacin damina, inda ruwa ke ƙaruwa a kowane lokaci.
Dr Hambali, wanda ya isa wurin da abin ya faru, ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Wasu daga cikin mazauna yankin da Rediyon Najeriya ta tattauna da su, sun nemi gwamnatin ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace, tare da inganta hanyoyin sufuri ta ruwa.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Taura ƙaramar hukumar kwale kwale
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba.
“Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi sun dogara ne da bayanai marasa inganci da tunanin cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne,” in ji Idris.
“Waɗannan miyagu (’yan ta’adda) ba su ware addini ɗaya ba, suna kai wa Kiristoci da Musulmai hari musamman a Arewacin ƙasar nan.”
Ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai da ke zaune lafiya tare, kuma irin waɗannan rahotanni na ƙarya na iya haddasa rikici da tayar da fitina.
“Keɓe waɗannan hare-hare da sunan wani addini abu ne mai hatsarin gaske. Najeriya ƙasa ce wadda mutane suka yadda da juna inda mutane masu addinai daban-daban ke rayuwa cikin lumana,” in ji ministan.
Idris, ya ce gwamnati na ci gaba da inganta fannin tsaro, ciki har da samar da sabbin kayan aiki da haɗin kai mai ƙarfi tsakanin hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2009, Najeriya ke yaƙi da ta’addanci da ’yan fashin daji, kuma sauye-sauyen da aka yi kwanan nan sauke Hafsoshin Tsaro na nufin inganta tsaro.
Ministan, ya ƙara da cewa gwamnati tana amfani da hanyoyin zaman lafiya ta hanyar noman abinci, samar da ayyukan yi, da shirye-shiryen tallafa wa jama’a don rage talauci da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.