Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau
Published: 29th, July 2025 GMT
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.
Sakataren Gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar a Talatar nan.
Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a AlkaleriSanarwar ta ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa.
Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne.
Ya kuma yi kira ga sabon sarki ya dage wajen kira da samun haɗin kai da ci gaban masarautar Gusau da jihar, da ma ƙasar baki ɗaya.
Alhaji Abdulkadir zai ɗare karagar ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar, inda zai maye gurbin mahaifinsa, Marigayi Mai martaba Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025.
Sabon sarkin ne babban ɗan marigayin, kuma kafin naɗa shi sarki, shi ne Bunun Gusau.
Ana iya tuna cewa, a Juma’ar makon jiya ce aka samu rahoton rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Dokta Ibrahim Bello yana da shekara 71 da haihuwa.
Sarkin ya rasu ne a daren Juma’a 24 ga watan Yulin 2025 bayan doguwar jinya a wani asibiti da ke Abuja, babban birnin Nijeriya.
Sanarwar da gwamnatin Zamfarar ta fitar ta ce: “Rasuwar mai martaba babban rashi ne ga Jihar Zamfara da ma daukacin Arewacin Nijeriya.”
Gwamna Dauda Lawal ne ya jagoranci jana’izar sarkin a Babban Masallacin Juma’a na Kanwuri da ke birnin Gusau.
A watan Maris na 2015 aka naɗa marigayi Dokta Ibrahim Bello a matsayin sarkin Gusau na 15, inda ya maye gurbin ɗan’uwansa Alhaji Muhammad Kabiru Danbaba bayan rasuwarsa.
Marigayin ya bar mata da ’ya’ya sama da 20.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Abdulkadir Ibrahim Bello Sarkin Gusau Ibrahim Bello sabon Sarkin sabon sarkin
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu.
Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu, ne ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da takarda a wajen taron shekara-shekara na kungiyar Nigerian Institute of Management reshen jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka hada da gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanta.
Farfesa Chika ya bayyana cewa, gwamnati tarayya na da shirye-shiryen tallafi da dama da suka hada da na noma, kasuwanci da kuma koyar da sana’o’in hannu domin kara habaka tattalin arzikin ‘yan Najeriya da rage zaman kashe wando, da tayar da hankali musamman matasa a yankin.
Ya jaddada cewa dole ne gwamnatocin jihohi su tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da hukumominsu na jin dadin al’umma domin cimma burin shirye-shiryen.
A jawabinsa wajen taron, kwamishinan noma na jihar Sakkwato, Muhammad Tukur Alkali, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayo manyan Tan-tan na noma guda 250 da kayan aikin gona da darajarsu ta kai naira biliyan ashirin da biyu da miliyan dari daya (₦22.1bn), domin tabbatar da wadatar abinci.
A cewar Tukur Alkali, gwamnatin jihar ta hanyar shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma, ta samar da sama da ayyukan yi 2,700 a bangaren noma, abin da ke da tasiri mai girma wajen bunkasa noma mai dorewa da ci gaban ababen more rayuwa a karkara.
Daga Nasir Malali