‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
Published: 29th, July 2025 GMT
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 15 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Mu’azu Barga, a wani samame da aka lakaba wa suna “Operation Kukan Kura”.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Ya ce samamen, wanda dakaru na musamman suka gudanar a unguwannin Sheka, Ja’oji, da Kurna a ranar 26 ga Yulin 2025, na da nufin gano da kuma hana aikata laifuka, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun.
Kiyawa ya bayyana cewa, wadanda aka kama ‘yan tsakanin shekaru 14 ne zuwa 28, kuma an same su da wayoyin salula guda hudu da suka sace daga hannun mutane daban-daban.
“Wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata sata da fashi, musamman satar wayoyin salula,” In ji shi.
“Mu’azu Barga, wanda ake zargi da kasancewa barawo a lokuta da dama, yana daga cikin wadanda aka kama. Ana danganta shi da laifukan fashi da makami, da kuma. jagorantar hare-hare masu tayar da hankali da fada tsakanin kungiyoyin daba a cikin birnin Kano.”
Kiyawa ya kara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ayyana yaki da duk wani nau’in laifi na daba, tare da jaddada kudurin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya bayyana godiyar rundunar bisa goyon bayan jama’a, tare da yin kira da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi da aikata laifi, a ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Abdullahi Jalaluddeen
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa.
A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa.
Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta a manyan teburan yanke shawara da ke tsara makomar al’ummarmu.”
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan kiraye-kirayen da aka yi daga sassa daban-daban na mazabarsa, tare da yabawa irin sha’awar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka nuna wajen yin aiki tare da shi domin kawo “ci gaba mai tarihi da ban mamaki” a yankin.
Sanata Katung, yayin canza shekan tare da Hon. Daniel Amos da wasu abokansa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya nuna gamsuwa da “ayukan ci gaban” jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Kudu, yana mai cewa suna nuna adalci, daidaito, da ci gaba.
Ya ce, “Zamanin warewa da nuna bambanci, musamman a baya-bayan nan, yana gushewa, kuma ana maye gurbinsa da gwamnatin da ke da manufa da haɗin kai.”
“Saboda haka muna matsawa gaba domin tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun dore kuma sun yadu zuwa sauran al’ummomi da dama a yankin,” in ji shi.
Sanatan ya kuma roƙi abokai da abokan aiki da ba su goyi bayan wannan mataki nasa ba, da su mutunta ra’ayoyi daban-daban, tare da kaucewa barin siyasa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Ya ambaci kalmar Thomas Jefferson da cewa, “Ban taɓa ɗaukar bambanci a ra’ayi na siyasa, addini ko falsafa a matsayin dalilin janye ƙauna daga aboki ba.”
“A tare, mu ci gaba da zama ɗaya a manufa, mu dage da fata, kuma mu mai da hankali wajen samar da makoma mafi kyau ga al’ummar Mazabar Kaduna ta Kudu.”
Sanata Katung ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiki don haɗin kai da cigaba.
Daniel Karlmax