Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma
Published: 29th, July 2025 GMT
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da fara karɓar dalibai a sabbin darussa guda shida a fannin noma a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a shekarar karatun 2025/2026.
Za a gudanar da shirye-shiryen ne a sabuwar Tsangayar Noma da aka kafa a garin Malam Sidi da ke Karamar Hukumar Kwami.
A ranar Litinin bayan taron majalisar gudanarwar jihar, Kwamishinan Noma da Kiwo, Barnabas Malle, ya bayyana cewa an amince da fara aikin sabuwar tsangayar aikin nomar ce ranar 21 ga Watan Mayu, 2025.
Sabbin darussan da aka amince da su sun haɗa da digir a bangaren Noma, Digiri a bangaren Gandun Daji da Dabbobin Jeji, Digiri a Kimiyyar Noma da Digiri a Kimiyyar Kasa, sai Digiri a fannin Tattalin Arzikin Noma.
Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a AlkaleriBarnabas Malle ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware filin gona mai girman hektar 365 a Garin Tafida da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba, domin bincike da aikin gwaji na ɗalibai.
Ya kara da cewa ana kokarin samun ƙarin fili a Garin Kurugu da ke Karamar Hukumar Kwami, don fadada ayyukan kwalejin a nan gaba.
Kwamishinan Ilimi Mai zurfi, Shettima Gadam, ya kuma tabbatar da cewa NUC ta ba da cikakken izini ga jami’ar don fara daukar daliban ne a wadannan darussa daga shekarar karatun 2025/2026.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami ar Jihar Gombe
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya ta ba wa Habasha kyautar iri da itatuwan cashew 100,000
Gwamnatin Najeriya ta ba wa ƙasar Habasha kyautar itatuwan cashew guda 2,000 da kuma irin cashew guda 100,000.
Najeriya ta bayar da kyautar irin ne a wani bangare na yunƙurin taimaka wa ƙasashen biyu wajen samar da abinci mai yawa da kuma ƙarfafa dangantakarsu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayar da wannan kyauta, da za ta iya shuke ƙasa mai fadin hekta 600.
Shettima ya bayar kyautar ce a lokacin da ya isa birnin Adis Ababa, babban birnin kasar, domin halartar Babban Taron Majalisar Xinkin Duniya Kan Tsarin Abinci.
Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir Matsalar Lantarki: Ga tsada ga rashin wuta An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a NejaMinistan Harkokin Noma na Habasha, Dakta Efa Muleta Boru, ya karbi kyautar, a matsayin wani bangare na shirin ƙasashen biyu na taimakon juna a fannin noma.
A watan Yuni na 2025, kasar Habasha ta ba wa Najeriya itatuwan avocado da na kofi.
Wannan kokari yana goyon bayan shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta noma a Najeriya.
Haka kuma yana nuna cewa Najeriya na son amfani da “Diflomasiyyar Juyin Juya Halin Kore” don gina kyakkyawar dangantaka da sauran kasashe tare da magance matsalolin samar da abinci.
Mataimakin Shugaban Kasa zai gana da sauran shugabannin duniya a taron domin tattauna yadda za a inganta samar da abinci a duniya. Zai kuma halarci wasu tarurrukan don musayar ra’ayoyi da kulla kawance.