Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Idan aka maimaita ta’asar kai hari kan Iran, za ta mayar da martani ta hanyar da ba za a iya boyewa ba

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani kan barazanar da jami’an Amurka suka yi a baya-bayan nan, inda ya ce idan aka sake kai hari kan Iran, za ta mayar da martani mai tsauri wanda ba zai yiwu a iya boye ba.

Araghchi ya kara da cewa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin din nan cewa: Iran, kasar da ke da al’adun gargajiyar da ta shafe shekaru dubu bakwai na wayewar kai, ba za ta taba mika kai ga barazana da tsoratarwa ba. Iraniyawa ba su taba mika kai ga kasashen waje ba kuma ba su bukatar komai sai girmamawa.

Ya ci gaba da cewa: “Iran ta san hakikanin abin da aka yi mata da kuma abin da makiya suka fuskanta a lokacin farmakin da ‘yan sahayoniyya da Amurka suka yi a baya-bayan nan, ciki har da yawan munanan hare-haren da ta kai a matsayin daukan fansa wadanda ake ci gaba da boyewa. Don haka idan makiya suka sake kuskuren kai hari kan Iran, babu shakka zasu fuskanci martani mai gauni da ba zai yiwu a iya boyewa ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan

Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.

A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.

Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ