Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
Published: 29th, July 2025 GMT
Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu.
A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci.
Haka nan kuma ya ce; Daga cikin manufofin da HKI ta Shata cewa za ta cimmawa a yayin yakin, shi ne samar da sauyi a cikin wannan yankin, shi ya sa da dama daga cikin hukumomin kasashen larabawa su ka fahimci cewa raunana Iran yana nufin raunana kasashensu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.
A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki.
Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin Hamas sun fahimci bukatar neman cimma muradun al’ummar Gaza da ake zalunta ta hanyar da ta dace, kuma ba sa bukatar shiga tsakani na bangarori na uku dangane da hakan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya yi la’akari da katsalandan din Iran a cikin shawarwarin da suka dace da cewa ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa irin wadannan zarge-zarge wani nau’i ne na neman tauyaye hakki da gujewa hakkin da ya rataya a wuyar mutum da kokarin Amurka na gujewa duk wani mugun aiki da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aikita kan al’ummar Falasdinu, da suka hada da kisan fararen hula 60,000 da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara da kuma killace Zirin Gaza tsawon watanni. Da hana shigar agajin jin kai da kuma kashe fararen hula da ke fama da yunwa da kishirwa a tarkon kisa a wuraren da ake kira cibiyoyin rarraba kayan agaji da wata cibiyar Amurka ta kafa.