Yadda Za Ki Hada Funkasonki
Published: 1st, June 2025 GMT
Za ki samu fulawa kamar gwangwani uku, ki zuba a roba sannan ki zuba suga kamar babban cokali biyu, sai gishiri rabin karamin cokali sai yis babba cokali daya, sai ki zuba ruwan dumi kofi daya da rabi, ki kwaba shi ki jujjuya shi ko ina ya hade, ki dan bubbuga shi kamar na minti uku haka, daga nan sai ki rufe shi ki kai shi rana domin ya taso.
Sai ki hada miyar da za ki ci da shi
Ki samu alayyahi da tattasai da dan tumatur idan kina so da taruhu da man, albasa:
Ki soya manki da albasa sannan ki zuba kayan miyan wanda dama kin jajjaga su, ki soya sai ki zuba magi, gishiri, kori, sannan ki kawo namanki ki zuba ki jujjuya shi,
Idan suka soyu, bayan sun soyu sai ki kawo alayyahinki wanda dama kin yanka shi kin wanke shi ki zuba ki ci gaba da juyawa, idan suka hade jikinsu sai ki rufe ki bar shi ya dan yi minti biyar haka kafin nan alayyahun ya dahu. Ita wannan miyar ba’a samata ruwa. A ci dadi lafiya.
Sannan kwabun funkason ya tashi, sai ki dakko shi ki zuba baikin fauda ki bubbuga shi saboda iskar ta fita, sai ki dora mai a wuta, wasu suna fadada shi da hannu, wasu kuma suna samun murfin wani abu haka mai fadi su yi da shi ko filat haka su rika zubawa suna fadadawa sannan su jefashi a cikin mai, za ki ga yayi ja shin e ya soyu, sai ki juya saman shima ya soyu haka za ki yi har ki gama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Cilla Tauraron Dan’adam Mai Suna Nahid-2 A Yau
JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kombon kasar Rasha a wannan cillawar ta isar da taurarin dan’adam da dama zuwa sararin samaniya. Banda tauraron dan’adam na kasar Iran ita ma kasar Rasha tana da taurarin dana dam guda biyu a cikin kumbon wato Ionosfera-M3 da M4, sannan da wasu 18 na wasu kasashe.
Kafin haka dai wannan kumbon na kasar Rasha ya taba aika taurarin dan’adam na kasar Iran guda 3 wato Khayyam, Parsa -1 da kuma hudhod.
Manufar cilla Nahid -2 dai shi ne kyautata harkokin sadarwa na JMI a sararin samaniya. Kuma kamfanonin gina taurarin yan adama a cikin kasa ne suka hada kai don ganin ya kammala.