2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
Published: 15th, October 2025 GMT
Ya ce manufofi da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata sun ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwa game da tattalin arziƙin ƙasa da tafiyar da gwamnati, abin da ya sa zai yi wuya a kayar da shi a 2027.
“Babu wani ɗan siyasa a yau da zai iya ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ƙara da cewa shugabannin ƙungiyoyi daga dukkanin shiyyoyi shida na ƙasar nan sun halarci taron, ciki har da wasu da suka zo daga Biritaniya.
Bwala, ya bayyana cewa taron ba yaƙin neman zaɓe ba ne, amma wata dama ce don gina kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da abokan hulɗa na ƙasa.
“Wasu mutane suna jiran lokacin zaɓe kafin su nemi ƙungiyoyi, amma wannan ba daidai ba ne. Ba kayan aiki ba ne, abokan tafiya ne, dole su kasance cikin abin da gwamnati ke yi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan taruka za a shirya su a Biritaniya, Amurka da Kanada don tattaunawa da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da kuma yaɗa bayanai game da nasarorin gwamnatin Tinubu.
Bwala, ya bayyana cewa Fadar Shugaban Ƙasa tana shirin gudanar da babban taron tattaunawa a watan Nuwamba, inda dukkanin ƙungiyoyi za su haɗu domin nazarin dabarunsu da kuma kimanta yadda gwamnati ke aiki.
Ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ta fara aiwatarwa sun fara bayar da sakamako a fannoni daban-daban kamar makamashi, noma, ayyukan gina ƙasa da samar da ayyukan yi.
“Mun riga mun fara ganin sakamako. Idan muka je fagen aiki, za mu ga ci gaba a bangaren tattalin arziƙi, tsaro, ilimi da noma. Waɗannan ƙungiyoyi za su ci gaba da yaɗa wannan saƙo,” in ji shi.
Shi ma tsohon ɗan majalisa, Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, wanda ya halarci taron, ya yaba wa jagorancin Tinubu.
“Ko mutum ya so ko ya ƙi, Shugaban Ƙasa zai sake lashe zaɓe a 2027. Ba mu kai inda muke so ba tukuna, amma muna cimma nasara. Shugaban Ƙasa na yin duk abin da zai yi don kawo ci gaba,” in ji shi.
Agbonayinma, ya kuma yaba da cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ba da damar a saki maƙudan kuɗaɗe don jihohi su inganta ci gaban al’umma a matakin ƙasa.
Dukkanin masu jawabin sun buƙaci ƙungiyoyin su ci gaba da yaɗa manufofin gwamnati da kuma tabbatar da haɗin kai tsakanin yankuna da jam’iyyu.
Bwala, ya kuma buƙaci magoya bayan Tinubu su ci gaba da nuna goyon baya da ƙauna ga Shugaban Ƙasa.
“Shugaba Tinubu ya yi abin da ya cancanci ba kawai goyon bayan jama’a ba, har ma da soyayya da jajircewarsu don ci gaba da abin da gwamnatinsa ta fara,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa da gwamnati
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh
Shugaban kasar Amurka Donal Trunp ya isa HKI a safiyar yau Litinin, inda ake saran zai yi jawabi a majalisar dokokin HKI, kafin ya wuce zasu Sharm sheikh na kasar Masar inda zai halarci bikin sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da kuma HKI wanda aka fara aiki da shi a wannan makon.
Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto hotunan bidiyo kai tsaye daga Telaviv a lokacinda jirgin shugaban kasar ya sauka, sannan shuwagaban HKI da kuma firai ministan HK Benyamin Natanyahu ne suka tarbe shi a tashar jiragen sama na Bengerion.
Shugaban ya iso HKI a dai dai lokacinda kungiyar Hamas ta mika fursinonin HKI 7 ga kungiyar Red Cross a zirin Gaza. Wanda daya ne daga cikin matakan aiwatar da yarjeniyar sulhu a HKI .
Tun 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne har zuwa watan octoban shekara ta 2025 sojojin HKI sun kashe Falasdinawa kimani 70,000 tare da tallafin Amurka da kuma kasashen yamma wadanda suka hada da Burtania, Jamus da Faransa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini October 13, 2025 Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal October 13, 2025 Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Bayyana October 13, 2025 Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci