Shugaban Kasar Amurka Ya Kara Yawan Kasashen Da Ya Sa Wa Takunkumin Shiga Amurka
Published: 17th, March 2025 GMT
Shugaban kasar ta Amurka Donald Ttump ya kara yawan kasashen da ya sa wa takunkumin shiga cikin Amurka zuwa kasashe 43.
Daga cikin kasashen da ya sa wa sharuddan shiga cikin kasar Amurka sun hada guda 11 da su ne; Somaliya, Sudan, da Libya. Sai kuma Afghanistan, Cuba, Iran, Korea Ta Arewa, Syria, Venezuela da kuma Yemen.
A lokacin zangonsa na farko Trump matakin nasa ya ja hankalin duniya saboda yadda ya hana ‘yan hijira daga kasashen Iraki, Libya, Somaliya, Sudan da Yemen shiga cikin kasar.
An kalubalanci matakin na shugaban kasar Amurka a wancan lokacin a kotu saboda yadda ya shafi mafi yawancin kasashen musulmi.
Bayan da Joe Biden ya zama shugaban kasa ya soke wancan matakin na Donald Trump a 2021.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.
M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.
Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.
Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”
Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.
Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.
Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.