Maggi Ya Kaddamar Da Wasanni Na Musamman Domin Watan Ramadan
Published: 17th, March 2025 GMT
Wasan na tare da jarumai da suka hada da Rekiate Ibrahim-AttahRekiya Attah, Ramadan Booth, Rabiu Rikadawa, da sauran jarumai. ‘MAGGI Tales of Ramadan’ yana kunshe da darussa masu kayatarwa da aka tsara na mako 6 wanda zai fara daga farkon watan Ramadan. A yayin kallon wasan za a fuskanci muhimman abin da zai karfafa soyayya a tsakanin al’umma.
A kowanne shafi na labarin zai fito da cikakken abubuwan da suke tattare da darussan watan Ramadan a tsakanin al’umma gaba daya musamman ganin yadda aka kama baki da rana har aka zo yin buda baki da kuma lokacin da yin sahur.
A jawabinta, shugabar vangaren kula da sarrafa MaGGI na kamfanin Nestlé Nigeria, Mrs Rahamatou Palm-Zakari ta bayyana cewa, “Ramadan lokaci ne na rarraba abin da aka mallaka cikin jin dadi da annashuwa a tsakanain al’umma, kuma mun fara wannan taarin ne fiye da shekara goma da suka wuce. Za kuma mu ci gaba da tallafa wa iyalai a cikin al’umma kamar yadda muka saba a baya
Mun kuma yi alkawarin tattaro mutane daga sassan kasa wuri daya, tabbas MAGGI ya yi imanin zaburar da mtane donm su nuna soyayya a tsakanin su musamman wanna lokaci na Ramadan.
MAGGI na daga cikin abubnwan alfarma da kamfanin Nestlé ke sarrafawa. Muna kuma alfahari da cewa al’umma dama har ma da wadanda ba a haifa yanzu za su ci gaba da amfana da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Za a aurar da marayu 200 a Zamfara
Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu.
Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar da ke Gusau.
Ya ce an gudanar da cikakken bincike da tantancewa kafin zaɓar waɗanda za su ci gajiyar shirin, domin tabbatar da cewa auren ya kai ga mutanen da suka fi buƙatar taimako na haƙiƙa.
Sakataren ya ƙara da cewa, hukumar za ta ba wa amaren kayayyakin tallafi da kayan amfani na gida domin taimaka musu su fara sabuwar rayuwarsu cikin sauƙi da kwanciyar hankali.