Dakta Umar Kabir Yusuf-Bakatsinen da ya kirkiro manhajar Masjid Suite da ke sada zumuncin hada masallaci da masallata
Published: 15th, October 2025 GMT
Dakta Umar Kabir Yusuf-Bakatsinen da ya kirkiro manhajar Masjid Suite da ke sada zumuncin hada masallaci da masallata
Daga Ibrahim B. Surajo
Dakta Umar Kabir Yusuf matashin manazarci ne dan asalin Jihar Katsina da yake zaune a kasar Amurka wanda ya kirkiri wata manhaja mai suna Masjid Suite. A cikin hirar da ya yi da Jaridar Aminiya matashi ya bayyana abin da ya sa ya kirkiri manhajar da kuma da ayyukan da take yi.
Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Ko za ka fada mana wacce manhaja ce ka kikira?
Sunan manhajar Masjid Suite, wacce ake saukewa a wayar hannu. Kuma na kirkire ta ne saboda saukake sadarwa a tsakanin masallaci da masallata musamman a nan kasarmu Nijeriya da sauran kasashe Afirka, kamar yadda ake da irin wadannan manhajojin a kasashen da suka ci gaba kamar kasar da nake da zama wato kasar Amurka. Manhaja ce da ake amfani da iya a wayar salula.
Ka ce manhajar tana sadar da alaka tsakanin masallaci da masallata, ko za ka yi mana cikakken bayani abin da hakan ke nufi?
E, ita wannan manhajar da farko dai tana sadar da masallaci da masallatansa ta hanyar tunatar da lokacin yin salloli. Wato idan lokacin daya daga cikin sallolin nan biyar da muke a rana, manhajar za ta tunawa mai amfani da ita ta hanyar kiran salla.
Haka kuma masallaci zai iya ba da sanarwa ta daurin aure ko jana’iza ga masallata ta hanyar tura masu da sako wanda idan suka bude manhajar za su gani. A maimakon a da za ka ga sai mutum ya zo masallaci salla, in an gama sallar ka ji an sanar da cewa akwai jana’izar da za a yi. Wanda ka ga wani da bai fito da shirin zuwa jana’iza ba ko kuma yake da wani muhimmin wurin zuwa dole zai wuce ba zai samu tsayawa a yi jana’izar da shi ba.
Sannan masallaci zai iya shirya taro ko wani karatu ya sanar da masu zuwa salla a masallacin kai tsaye ta hanyar wannan manhaja.
Bugu da kari kuma masallata na iya tura wa masallaci gudunmawar kudi kai tsaye da duk inda suke ta hanyar wannan manhaja ba tare da sun je masallacin ba.
To ta yaya masallata ke iya samun wannan manhaja?
Kamar sauran manhajoji, za a sauke wannan manhaja ne daga Google store sannan a yi rajistar suna da masalacinka wato wanda kake salla. Kuma za ka iya yin rajistar masallaci fiye da daya. Sannan sai ka sanya adireshinka da jiharka da ma unguwarku.
Idan kuma kai limami ne za ka yi rajistar masallacinka ne ta hanyar shiga kofar manhajar ta Admin wato masu kula da masallacin. Daga nan za ka ga yadda za ka iya sanya sanarwa ko tabbatar da karvar wata gudunmuwa da wani ya aiko wa masallacin.
To me ya ja hankalinka har ka kirkiri wannan manhaja?
Kamar yadda na fada a baya ganin yadda ake samun tsaiko wajen isar da sanarwa a tsakanin masallata da masallaci shi ne babban dalilina na kirkiro ta. Wato dai saboda sauwake zumunci da sadarwa a tsakanin masallata da masallatan da suke salla. Musamman ta yadda mutane za su iya ba da gudunmuwar kudi a asirce ga masallatai ba tare da wani ya sani ba.
Shin sai an biya kudi za a iya amfani da wannan manhajar?
Na kirkiri wannan manhaja ba don nemna kudi ba don haka ba sai an biya kudi ba ake amfani da ita.
Ko me ya banbanta wannan manhaja da sauran manhajojin da ake da su irin ta?
Babban abin da ya banbanta manhajarmu da sauran shi ne cewa, ita wannan manhajar kowane masallaci day a yi rajista shi ne zai sanya lokuttan sallarsa. Kuma idan lokacin kiran sallar ya yi sai mabiyansa su ga alamar tunatarwa ta hanyar kiran sallah. Ba kamar sauran manhajoji ba da suna amfani da lokacin kiran sallah na bai daya wanda suke dauka a kalanda.
Ko ka yi hadin kwiwa da wasu kungiyoyin addini da ken an Nijeriya don ganin ka samu masallatai da za su yi rajista da wannan manhajar?
Lallai na nemi hadin gwiwar kungiyoyi addini na kasar nan kuma tuni na zauna da shuwagabannin wasu daga cikin su mun tattauna na yi masu bayani game da yadda manhajar ta za ta taimaka masu da kuma irin yadda take aiki.
To wane irin tarba ka samu daga gare su?
A gaskiya dukkan su sun yi maraba da manhajar kuma sun kara ba ni shawarwari tare dab a ni tabbacin samun cikakken goyn bayansu.
Shin wannan it ace manhaja ta farko da ka kirkira?
E, a matsayina na ni kadai zan iya cewa wannan it ace ta farko. Duk dai da yake a wurin aikina can a Amurka na taimaka wajen kirkira wasu manhajoji da ake amfani da su a vangaren kiwon lafiya.
Ko dama a fannin fasaha da kirkire-kirkine ka yi karatunka?
E, kai tsaye ba zance a wannan fanni na yi karatu ba. Domin na yi digirina na uku ne a fannin kiwon lafiya. To sai dai na yi karatun kirkire-kirkiren na fannin aikin lafiya. Kuma wurin da nake aikin wuri ne da ake bincike da kuma kirkire-kirkire da suka shafi harkar kiwon lafiya, wanda a halin yanzu ma ni ne shugaban sashen bincike a wurin da ke kasar Amurka.
Kai tsaye wace shawara za ka ba wa matasa masu irin wadannan fasahohi a Nijeriya?
Shawarar da zan basu ita ce su ci gaba da jajijircewa wajen ganin idan suna da wata fasaha da take a rubuce ko a cikin kansu su tabbatar sun doge a kan sai sun aiwatar da ita a zahiri. Domin ita basira indai har ba a aiwatar da ita bat a zama bat a da amfani. Don haka duk mai wata basira ya dage ya ga ya fara aiwatar da ita a zahiri daga nan kuma zai iya neman kungiyoyi ko kamfanonin da suke tallafa wa masu basira don ganin ya samu tallafin da ya kamata.
Wane kira za ka yi ga gwamnati don ganin ta tallafa wa matasa masu basirar kirkire a Nijeriya?
Kiran d azan yi wa gwamnati shi ne su mayar da hankali wajen inganta harkar ilimi musamman vangaren kimiyya da fasaha wanda da su ne kasahen da suka ci gaba suka yi mana fintinkau. Sannan ya kamata duk wani mutum da aka gani yana da wata basira ta musamman musamman ma a fannin kirkire-kirkire ya ya dace a tallafa masa har ya ga ya cimma burinsa. In ma ya kama ne a dauki nauyinsa to haka ya kamata a yi.
Ko sai kana da data a waya zai iya amfani da manhajar?
E, kusan haka, amma dai mun tsarata ta yadda ba za ta ja data din sosai ba. Saboda haka da zarar ka kunna datar ka za ta yi amfani da ita kadan kuma za ka iya samun sanarwar masallacinka ta wannan rana. Daga bisani kuma washe gari sai ka sake kunnawa ka kasha idan kana son samun sanarwar wannan raranar.
Shin a cikin wane harshe ka tsara wannan manhajar?
A halin yanzu dai za a iya amfani da ita da harsunan Hausa da Ingilishi da Larabci kuma muna nan muna kokari kara Yarbanci da harshen Ibo da Faransanci.
Ganin cewa kai mazaunin kasar Amurka ne, wace shawara za ka ba wa ‘yan Nijeriya musamman masu sanya kansu cikin hadari ta kokarin hijira daga Nijeriya zuwa kasashen Turai ta varauniyar hanya sahara?
To duk da yake dai Hausawa na cewa wai abin day a koro vera daga rami ya fada wuta ya fi wutar zafi. Amma dai duk da haka bai dace mutane su dinga sanya kansu cikin irin wannan hadari ba, abin day a kamata ga duk mason zuwa cirani ko jin hijira zuwa kasashen Turai shi ne ya yi kyakkyawan tanadi na kudi don kaucewa fadawa cikin hadarin da ka iya ma zama sanadin halakarsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: a wannan manhaja wannan manhajar kasar Amurka kiran salla
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk
Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba.
Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.”
Trump ya kara da cewa shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci makamai masu linzami na Tomahawk lokacin da suka tattauna sabbin makamai ga kasar ke bukata ta wayar tarho a ranar Asabar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci