2025-10-13@17:53:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6883
«Tsamiya»:
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House jiya litinin cewa, yana fatan samun zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya. Trump ya sanar da kaddamar da abin da ya kira “Ka’idojin Zaman Lafiya” a hukumance, tare...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nemi afuwar firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a ranar Litinin din nan kan harin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kai kan Qatar a baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar wani jami’in tsaron Qatar, kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa Axios. An bayar...
Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, wanda ya ziyarci kasar Lebanon domin halartar bikin zagayowar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem. Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah...
Masana’antar kera makamai ta srael, wacce aka dade ana daukarta a matsayin daya daga cikin manyan ginshikan tattalin arzikin gwamnatin da kuma wani muhimmin makami na amfani da siyasarta, a yanzu na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba. A cewar Pars Today, yayin da yake ambato Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, yayin...
Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-ker ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna sun tsunduma yajin aiki. Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere (ASUP) reshen makarantar ta fara yajin aikin ne daga yau Talata, 39 ga Satumba, 2025. Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne bayan zaman da ta yi da wakilan gwamnatin jihar, inda...
An sanar da wannan matakin ne a yau 29 ga watan Satumba, 2025 a karkashin dokokin FIFA, amma kuma har yanzu SAFA suna da kwanaki goma domin daukaka kara a gaban kwamitin daukaka kara na FIFA. Tawagar Afirka Ta Kudu wadda Hugo Broos ke jagoranta a halin yanzu suna kan gaba a rukuninsu na...
Yau Litinin ofishin ‘yan jarida na kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai don bayyana nasarorin da Sin ta samu a fannin ban ruwa a lokacin “shirin raya kasa na 14 na shekaru biyar” . Minista mai kula da harkokin ban ruwa Li Guoying ya bayyana cewa, tun daga farkon shirin, Sin ta fara...
Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya. Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari...
A taƙaitaccen hukuncin da ya yanke kan ƙarar, Mai shari’a Subilim ya bayyana cewa, ci gaba da yajin aikin zai lalata kasuwancin matatar da gurgunta mafi mahimmancin ayyukan ci gaban tattalin arzikin al’ummar Nijeriya. Alƙalin kotun ya ce, dokar hana ci gaba da yajin aikin za ta ci gaba da aiki har tsawon kwanaki...

Sin Da AU Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna A Fannin Hadin Gwiwar Raya Kimiyya Da Fasaha
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya bayyana cewa, bin wannan ƙa’idojin yana da matukar muhimmanci domin bai wa hukumar damar tattara sahihin jerin sunayen maniyyata da kuma tura dukkan kuɗaɗen zuwa ga hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) a kan lokaci. Ya shawarci maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu da su miƙa takardunsu na tafiya cikin gaggawa. Daga...

Masana’antar Raya Al’adu Ta Sin Ta Samu Ci Gaba Bisa Daidaito Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Karo Na 14
Masana’antar raya al’adu ta kasar Sin, ta samu ci gaba bisa daidaito yayin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, wanda aka gudanar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. A cewar mataimakin ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Lu Yingchuan, a shekarar 2024, darajar jimillar kadarorin sashen ta kai...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya. Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu FERMA ta ƙaddamar da...
Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. ASUU ta bayar da wa’adin...
Idan dai ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba buƙatar ƙungiyar ASUU, a wani yunƙuri na tabbatar da ci gaban jami’o’in. Sai dai har yanzu kwamitin bai fitar da wata sanarwa ko sakamakonsa ga jama’a...
Da yammacin yau Litinin ne ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taron nazari karo na 22, kan yadda za a sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar. Yayin da ya jagoranci taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada cewa, “Ya kamata mu...
Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda...
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu domin tsunduma yajin aiki muddin ta ci gaba da sakaci kan wasu buƙatu da take nema a biya. A sanarwar gargaɗi da ASUUn ta fitar yau Litinin, ta ce daga jiya Lahadi, 28 ga watan Satumba, za ta bai wa gwamnatin...
Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya, wato PENGASSAN, ta fara yajin aiki a faɗin Nijeriya daga daren Litinin, 29 ga Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan umarnin da shugabancin ƙungiyar ya bayar tun ranar Lahadi, inda aka umurci mambobi da su tsaida aiki a dukkan kamfanoni da cibiyoyi da hukumomin da...
’Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 165.4 a watan nan na Satumba a Jihar Kano. Daga ciki, jami’an rundunar sun kama kwayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 82.7 a unguwar Rimin Auzinawa, suka mika ga Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin kammala bincike da gurfanarwa...
Jami’an tsaron kasar Burtania sun kama George Gallaway da matar a birnin londan bayan sun shigo kasar daga kasar Rasha a ranar Asabar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa Gallawy da matarsa sun shahara da goyon bayan gwagwarmayan falasdinawa da kuma kiyayya ga HKI. Kafin haka gwamnatin kasar Burtania ta amince...
Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi...
Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Ɗangote don a sasanta a yau. Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan ƙwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Ɗangote ta salami ma’aikata fiye...
Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar. A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na...

Ana Hasashen Adadin Zirga-Zirgar Fasinjoji Yayin Hutun Bikin Tsakiyar Kaka Na Sin Zai Kai Biliyan 2.36
Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce adadin zirga-zirgar fasinjoji yayin hutun bikin tsakiyar kaka na Sin dake tafe nan da ‘yan kwanaki, zai kai kimanin biliyan 2.36. Da yake karin haske kan hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lahadin nan, mataimakin ministan ma’aikatar Li Yang, ya ce yayin kwanaki takwas...
Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga jimami bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda. An kama Salim mai shekara 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba. 2027: APC za ta ƙwace...
Wani jami’in ’yan sanda a Jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro. Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro. Limami ya rasu a hannun ’yan sanda a Kano...
Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti...
Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga jimami bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda. An kama Salim mai shekara 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba. 2027: APC za ta ƙwace...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Rashin Amincewa Da Duk Wani Takunkumi Kan Iran
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu...
Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne...

Kasashe 77 Ne Na Duniya Suka Fice A Lokacin Jawabin Fira Ministan Isra’ila A Taron Majalisar Dinkin Duniya
Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kasashe 77 ne suka fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benyamin Netanyahu ke jawabi ga babban zauren Majalisar a birnin New York....
A yau Lahadi ne aka gudanar da biki mai taken “Bude sabon babi a sabon zamani: Bikin zurfafa hadin gwiwa tsakanin CMG da bangarori daban daban na Macao” a yankin Macao na kasar Sin. Shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG Shen Haixiong, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi....
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na Amurka, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA). Ya nufi Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutsche kan batutuwan haɗin gwuiwa da zuba jari a shirye-shiryen ci gaban Nijeriya. A yayin taron UNGA, Shettima ya samu...

Xi Ya Yi Kira Ga Makarantun Horar Da ‘Yan Jam’iyya Da Su Kara Azamar Kyankyashe Hazikai Da Gabatar Da Shawarwari Ga JKS
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS. Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya...
Dakarun Operation Haɗin Kai su kama wani mutum da ake zargi yana kai wa Boko Haram man fetur a Jihar Borno. Wanda aka kama, mai suna Thomas James, mai shekaru 54, an cafke shi ne ranar 23 ga watan Satumba a kusa da sansanin Forward Operating Base da ke Ngwom. PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki...
Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta fara yajin aiki saboda korar wasu ma’aikata a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas. Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce sun fara yajin aikin ne daga ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa...
Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki. Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun...
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa...
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa...
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi zargin cewa, cikin watanni shida, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya samu karin kaso daga gwamnatin tarayya fiye da yadda ya samu a cikin shekaru 8 da ya yi yana gwamna. Batun rabon kuɗaɗen wata-wata ga Jihohin dai ya zama abun muhawara a karkashin gwamnatin Shugaba...
Majalisar Dinkin Duniya ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai na karayar tattalin arziki bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar ƙarshe kan shirin nukiliyarta da manyan ƙasashen yammacin Turai. Birtaniya, Faransa da Jamus ne suka bijiro da batun maido da waɗannan takunkuman a taron kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda aka yi kan saɓa yarjejeniyar...
Kamaru Kasar Kamaru tana da alaka sosai da Isra’ila. Daraktan fannin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaron Kasashen Afirka da tsare-tsare a Geneba, Dabid Otto ya ce Isra’ila na kallon Kamaru a matsayin daya daga cikin kawayenta na kusa a Afirka. Ya ce “Kamaru ba za ta yi gangancin lalata alakar diflomasiyya da ke tsakaninta...
Firaministan Nijar Mahaman Lamine Zein ya yi Allah wadai da yadda kasashen ketare ke da hannu wajen tada zaune tsaye a yankin Sahel. Lamine Zein, ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar da a zauren babban taron MDD karo na 80 dake gudana a birnin New York. Nijar ta kuma yi Allah wadai da...
A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne suka jikkata yayin zanga-zangar ta nuna goyon bayan Falasdinu bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye a ranar Asabar....
Matatar Dangote ta janye ƙudirin dakatar da sayar da man fetur a naira, tana mai cewa abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala. Lamarin na zuwa ne ƙasa da kimanin sa’o’i 24 bayan matatar ta sanar da dakatar da cinikayyar man fetur da naira. Makon gobe za a...
Matatar Dangote ta janye ƙudirin dakatar da sayar da man fetur a naira, tana mai cewa abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala. Lamarin na zuwa ne ƙasa da kimanin sa’o’i 24 bayan matatar ta sanar da dakatar da cinikayyar man fetur da naira. Makon gobe za a...
Maude dan shekara 40, kwararren lauya ne, kuma haziki wanda ya kammala karatun digiri a fannin shari’a daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Shi mamba ne a kungiyar lauyoyin Nijeriya da kuma a Cibiyar Masu sasantawa ta Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...