An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda 29 a Borno
Published: 11th, November 2025 GMT
Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno.
A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya.
Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin Sashe na 2 na OPHK sun yi artabu da mayakan Boko Haram da ISWAP a Dutsen Kura, inda suka fatattake su bayan fafatawar da ta gudana har zuwa yankin Mangari.
Sanarwar ta bayyana cewa an gano mafakar ’yan ta’adda guda 11, sannan an kubutar da maza, mata da yara 86 da aka garkuwa da su.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai 73, jigidar harsashi 5, motoci 5, babura 5, kekuna 8 da kuma babura masu ƙafa uku guda 2.
A wani samame na daban a Mangada, dakarun sun kama mutum 29 da ake zargi da kai wa ’yan ta’adda kayayyaki, tare da kwace motocin ɗaukar kaya guda 2 da babura masu ƙafa uku cike da man fetur da man injin sama da lita 1,000.
Laftanar Kanar Uba ya ce an gudanar da duka ayyukan ba tare da asarar rai ko rauni a ɓangaren sojoji ba, inda babban kwamandan rundunar ya yabawa jarumtar dakarun tare da buƙatar su ci gaba da hana ’yan ta’adda samun damar shakatawa a duk faɗin yankin Arewa maso Gabas.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda jihar Borno yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji November 9, 2025
Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15 November 9, 2025
Daga Birnin Sin Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba November 9, 2025