Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe
Published: 11th, November 2025 GMT
Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe.
Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta.
John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a BornoMutumin da ake zargi da wannan aika-aikar mai suna Rabilu Sani, ɗan kimanin shekara 22, an gano cewa yana ɗauke da cutar kanjamau (HIV), kamar yadda mahaifin yarinyar ya tabbatar wa manema labarai.
A wata hira da aka yi da mahaifin ta ta wayar tarho, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin Jakusko tare da wanda ake zargi, inda likita ya gudanar da gwaje-gwaje, kuma sakamakon ya tabbatar da cewa mutumin na ɗauke da cutar HIV.
A halin yanzu, wanda ake zargi yana hannun jami’an ’yan sanda na Jakusko, inda ake ci gaba da gudanar da bincike, kamar yadda baturen ’yan sandan yankin ya bayyana wa manema labarai.
Ya ƙara da cewa da zarar an kammala bincike, za a miƙa wanda ake zargin ofishin su da ke Damaturu, fadar jihar, domin zurfafa bincike, kafin daga bisani a samu ƙarin bayani daga bakin kakakin rundunar a matakin jiha.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: fyaɗe Jihar Yobe yarinya
এছাড়াও পড়ুন:
Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata
Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba.
Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.
Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da wurin ya yi faɗa da mamacin kafin daga bisani ya yanke jiki ya faɗi ya mutu.
Matar tsohon Shugaban Ƙasa Shagari ta rasu EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jalloMajiyar ta ƙara da cewa an garzaya da mutumin asibiti domin ba shi agajin gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Rahotanni sun ce an kama wani mutum daga cikin gidan matan da ake zargi da hannu a lamarin, kuma rundunar ’yan sanda ta jihar ta ta fara bincike a kai.
SP Grace Iringe-Koko ta kuma tabbatar da cewa an kama mutum ɗaya da ake zargi, kuma sashen ’yan sanda na Azikiwe ya miƙa shari’ar zuwa SCID domin gudanar da bincike mai zurfi.
Sai dai bayan faruwar lamarin, an lura dukkan ’yan mata masu zaman kansu da ke yawo a cikin da wajen gidan karuwan sun yi layar zana.