2025-05-02@05:16:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 448

«Kyautatawa»:

    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar da yake yi a Birtaniya. Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce ziyarar ta Wang Yi ta cimma nasara da kyawawan sakamako. Ya ce wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A...
     Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da  kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya...
    Kungiyar Hamas ta yi kira ga ƙungiyoyin duniya da su fitar da matsayinsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi don yin watsi da batun neman tilastawa Falasdinawa yin hijira daga Zirin Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira ga al’ummar Falastinu, al’ummar Larabawa da al’ummar musulmi da dukkan ‘yantattun kasashe a...
    An bude babban taron majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, watau AU karo na 46, a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda taron ya jaddada bukatar gaggauta karfafa kokarin da ake yi na bunkasa ci gaban nahiyar, da kwanciyar hankali. Taron na kwanaki biyu, wanda ya kunshi ministocin harkokin waje na mambobin kungiyar ta AU,...
    Duk da haka, da alama cewa, waɗannan binciken ƙila ba su da isasshen ikon gano bindigogin da suka ɓace.   A yanzu haka dai, kwamitin majalisar dattawa yana zaune a Abuja domin ci gaba da bincike kan lamarin.
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
    “Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A...
    Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta. Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada. Gwamnatin Kano...
    Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa....
    Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya...
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya.   Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar.   “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game...
    Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza. Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi...
    Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina...
    Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira. Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Aisha...
    Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da...
    Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaben 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ‘yan siyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. Fadar Shugaban kasa ta mayar da...
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a...
      Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu.   Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta...
    Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu a duk fadin duniya a cikin shekaru 4 masu zuwa saboda rashin samun tallafin Amurka a cikin shirin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayyana cewa, a...
    Firay Ministan HKI Banyamin Natanyahu ya bawa kasar Saudiya Shawara samarwa Falasdinawa kasa daga cikin hamada mai girma da take da shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka wa wata tashar talabijin ta HH a safiyar yau Asabar. Amma a maida martani ga Natanyahu, dan majalisar dokokin kasar...
    Dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan kasar Jordan da kasar Iraki domin yin Allah wadai da shirin shugaban Amurka Donald Trump na korar Falasdinawa daga yankin Gaza. Masu zanga-zanga a Amman babban birnin kasar Jordan, da kuma wasu garuruwan kasar Larabawa, sun yi zanga-zangar nuna adawa da shirin na tilastawa mazauna zirin Gaza...
    Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na...
    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe,...
    Ministan yaki na HKI Israel Kant ya umurci jami’an gwamnatin kasar su fidda wani tsari wanda zai bawa falasdinawa damar ficewa daga yankin Gaza a radin kansu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan ya na haka  bi sa umurnin da shugaba Trump na Amurka ya bayar na cewa ‘zai kwace Gaza’....
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar...
    Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan...
    Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) ofishin Kano ta kai ziyarar gani da ido ga hukumar samar da magunguna ta jihar Kano (DMCSA).   Wannan ziyarar alama ce ta farkon tsarin ba da izini ga DMCSA don zama cibiyar rarraba magunguna ta mega da cibiyar bada horo.   Jami’ar Jihar Kano mai kula da...
    Mataimakin shugaban kasar Iran kan al-amuran na Musamman Muhammad Javad Zareef  ya bayyana cewa tattaunawa kadai da Amurka, ba zai warware matsalolin Iran ba. Kamfanin dillancin labarum IP na kasar Iran ya nakalto Zareef ya na fadar haka a taron majalisar ministocin da aka gudanar a jiya Laraba  a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP...
    Shugabannan Palasdinawa daga cikin har da kungiyar Hamas da Jahadul Islami duk sun ki amincewa da shirin trump na sake kwace Gaza, kafin haka kuma shugaban ya ce dole Falasdinawa su daga yankin kafin ya kwace shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran  ya nakalto shuwagabannin Palasdinawan suna allawadai da shugaban, sun kuma kara...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewarsa ga manufar majalisar, ta bullo da tsarin bada tallafin sana’oi na mazabu ba tare da jinkiri ba. Shugaban Majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafi wanda wakilin mazabar Kanya a majalisar dokokin jihar,Alhaji Ibrahim Hashim...
    Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairu, 2025. Karin wa’adin na zuwa ne biyo bayan koke-koke da aka kai wa hukumar na a kara wa maniyyatan da suka gaza kammala biyan kudinsu a kan...
    Mutanen kasar Amurka sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da korar Falasdinawa daga Gaza ne, bayan taron da yan jaridu na Trump Da Natanyaho a birnin washintong a jiya Talata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zangar su na rera taken cewa “gaza ba na sayarwa bane”. Maganganun Trump a baya-bayan...
    Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da tsawaita wa’adin karɓar kuɗin aikin Hajjin bana. NAHCON ta ce daga yanzu zuwa 10 ga watan Fabrairu ƙofa a buɗe take ta ci gaba da karɓar kuɗin kujera ga maniyyatan da ke son sauke farali a bana. Jami’ar ABU da ke Zariya ta yi sabon shugaba An...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da asusun horar da ma’aikata ITF. Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun horas da ma’aikata na yankin arewa maso yamma, Malam Aminu Abdu a ofishinsa. A cewarsa, gwamnatin...
    Shugaba Bola Tinubu ya ƙi rattaba hannu kan ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Numan da ke Jihar Adamawa. Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wadda mataimakinsa, Benjamin Kalu ya karanta a yayin zaman majalisar na yau Talata. Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala...
    Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan  ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa;  A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara...
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta...
    HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan  yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin...
    Mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 13 suka jikkata a sanadiyyar wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da tireloli uku waɗanda suka yi karo da juna ’yar tazarar mitoci ƙalilan zuwa garin Agaie. Mai gari...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren  wurin shan shayi da taliya na zamani  a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.   Ta kara da...
    Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan...