Daga Usman Muhammad Zaria 

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanya da kudinta ya kai Naira Biliyan 14 a Karamar Hukumar Malam Madori, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa1 karkashin shirin sabunta kudurori na gwamnatin tarayya wato “Renewed Hope Agenda.

A yayin taron kaddamarwar, an kuma gabatar da sabbin motoci ga shugabannin jam’iyyar APC guda takwas da masu tallata jam’iyyar a mazabar Arewa maso gabashin jihar, wanda Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya dauki nauyi.

Wannan mataki na da nufin karfafa hadin kai a jam’iyyar da kuma tallata hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadin jihar.

A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar Sanata Ahmed Malam Madori na nuna biyayya, karamci, da sadaukarwa wajen ci gaban jam’iyyar APC. “Wannan babbar shaida ce ta jajircewar Sanata Malam Madori ga jam’iyyarmu”.

 

Haka kuma Gwamnan ya karfafa gwiwar sauran mambobi da su tallafa wa shirin ci gaba na Shugaba Tinubu karkashin ‘Renewed Hope Agenda.”

Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya bayyana cewa tallafin motocin na nufin bai wa mambobin jam’iyya damar yin ingantaccen aiki wajen tallata shirin ci gaba na Shugaban kasa da kuma Shirin Ci Gaba na Gwamna Namadi.

“Shugaba Tinubu da Gwamna Namadi sun kawo gagarumin ci gaba ga al’umma da ababen more rayuwa a Jigawa. An amince da kafa muhimman hukumomin tarayya, ciki har da Cibiyar Horar da ‘Yan Sanda a Kafin Hausa, Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Malam Madori, da Kwalejin Noma ta Tarayya a Kirikasamma,” in ji shi.

Ya jaddada ayyukan Gwamna Namadi na baya-bayan nan, ciki har da aikin hanyar kilomita 47 da ke hada Hadejia–Garun Gabas, inganta asibitoci, da farfado da cibiyoyin lafiya na farko.

Sanata Malam Madori ya kara da jaddada hadin kan masu ruwa da tsaki na APC a mazabar Arewa maso gabashin Jigawa, wanda ya hada da ‘yan majalisar wakilai guda uku, ‘yan majalisar jihar guda tara, shugabannin kananan hukumomi takwas, da ‘yan majalisar kananan hukumomi 85

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Gwamna Namadi

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu

Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba.

Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi.

Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra

Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445.

George Moghalu na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401.

Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban bankin Najeriya ne, ya lashe zaɓen ne domin yin sake mulkin jihar a karo na biyu.

Hukumar ta wallafa sakamakon zaɓen ne a shafin intanet na musamman mai suna IReV, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2022 ta tanada.

Tun da farko dai INEC ta sanar da sakamakon a hedikwatarta da ke Awka a hukumance, amma ta ce tana gudanar da lissafin ƙarshe na alƙaluman kafin ta ayyana Charles Soludo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Bitar sakamakon da hukumar ta fitar a hukumance ta nuna cewa ta hanyar lashe zaɓe a duk ƙananan hukumomi 21, Charles Soludo ya riga ya wuce ƙa’idar Kundin Tsarin Mulki don haka za a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Duk da cewa zaɓen ya kasance cikin kwanciyar hankali a faɗin jihar, akwai damuwa game da siyan kuri’u, yayin da hukumar EFCC ta ce jami’anta sun kama mutane uku da ake zargi da sayen kuri’u a lokacin zaɓen.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yarin Fika ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a Yobe
  • Yarin Fika ya sauya sheƙa PDP zuwa APC a Yobe
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar Yayin Daukar Ma’aikata
  • Kungiyar ‘Yan Dako Reshen Jigawa ta Kaddamar da Sabon Shugaba
  • Kungiyar Hadin Kai Ta Kafin Hausa Ta Horas Da Matasa 160 Sana’o’in Hannu
  • Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu
  • Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa