Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo
Published: 10th, November 2025 GMT
Bisa goron gayyatar da gwamnatocin kasashen Guinea da Saliyo suka ba shi, Liu Guozhong, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda kuma shi ne mataimakin firaministan gwamnatin kasar, zai kai ziyara kasashen Guinea da Saliyo daga yau Litinin 10 zuwa 16 ga watan da muke ciki.
Sannan, bisa gayyatar shugaban kasar Guinea Mamady Doumbouya, Mr. Liu Guozhong zai kuma halarci bikin kaddamar da mahakar karafa ta Simandou a kasar ta Guinea, a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping. (Lubabatu Lei)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025
Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025
Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025