Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali
Published: 10th, November 2025 GMT
Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum.
Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro.
Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe.
Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya.
Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin” mai alaka da alka’ida ce ta killace iyakokin kasar da ake shigar da kayan bukatuwar yau da kullum. A cikin watannin bayan nan an rika nuna fayafayen bidiyo na yadda ‘yan al’ka’idar suke kona jerin motocin jigilar makamashin da ake amfani da shi. A wasu yankunan kasar ma,kungiyar ta kone gidajen man fetur.
Kamfar makamashin da ake fama da ita a cikin kasar ya sam shugaban kasar Assimi Goita, ya yi kira ga al’ummar kasar da su rage yawan tafiye-tafiye akan Ababan hawa saboda a rage yawan bukatuwa da makamashin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Fara Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Sheikha Hind Bint Maktoum November 10, 2025 Zaben Iraki: Gwaji don ‘yancin siyasa da kawo karshen tsoma bakin Amurka November 10, 2025 Iran da Rasha sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa November 10, 2025 Iran ta nuna damuwa kan zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan November 10, 2025 Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa November 10, 2025 Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean November 10, 2025 Lebanon: Mutane 28 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila tun daga watan da ya gabata November 10, 2025 Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla November 10, 2025 Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan November 9, 2025 Kasashen (AES) za su hanzarta kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kamaru: Jagoran ‘yan Hamayya Chiroma Ya Bai Wa Gwamnati Sa’o’i 48 Da Ta Saki Dukkanin Wadanda Aka Kama Bayan Tsabe
Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.”
Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira ” Nuna wariya ta kabilanci.”
Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.”
A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%.
Shi dai Chiroma ya bayyana cewa shi ne wanda ya lashe zaben, illa iyaka mahukuntan kasar sun yi magudi ne da sauya alkaluman kuri’un da aka kada.
Wani rahoto na MDD ya ce; Jami’an tsaron kasar Kamaru sun kashe masu Zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben 48, yayin da mahukuntan kasar suke cewa mutane 5 ne su ka rasa rayukansu.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban kasa, inda ya yi kira da a kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake yi.
A karshen sakon nasa, Chiroma ya ce idan har ba a yi aiki da bukatar da ya bijiro da ita ba, to kuwa mutanen kasar za su yi duk abinda za su iya domin kwato da ‘ya’yansu da ake tsare da su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Jarida 44 Ne Su Ka Yi Shahada A Sansanonin Hijira Na Gaza November 10, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Isra’ila” A Yankin Saida November 10, 2025 Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali November 10, 2025 An Fara Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Sheikha Hind Bint Maktoum November 10, 2025 Zaben Iraki: Gwaji don ‘yancin siyasa da kawo karshen tsoma bakin Amurka November 10, 2025 Iran da Rasha sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa November 10, 2025 Iran ta nuna damuwa kan zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan November 10, 2025 Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa November 10, 2025 Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean November 10, 2025 Lebanon: Mutane 28 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila tun daga watan da ya gabata November 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci