Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn
Published: 11th, November 2025 GMT
Tawagar lauyoyin Trump ta ce an ɓata masa suna da mutunci, inda ta bayyana cewa BBC ta yi hakan ne don siyasa.
Trump ya taɓa shigar da ƙorafe-ƙorafe makamantan wannan a kan wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka, ciki har da ABC, CBS, da The New York Times, bisa zargin yaɗa labaran ƙarya a kansa.
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump bisa zargin kisan Kiristoci
A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa zargin gwamnatin kasar da kauda kai kan kisan da ake wa kiristoci a kasar.
Masu zanga-zanga a Kano, dake arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai da barazanar da kuma yin watsi da ikirarin na Trump na “kisan kiyashin Kiristoci.”
Masu zanga-zangar sun zargi Washington da amfani da addini domin tsoma baki da a cikin harkokin cikin gidan Najeriya, suna gargadin cewa duk wani matakin soja na Amurka zai keta hurumin Najeriya.
A ranar 1 ga Nuwamba, ne Trump ya ce ya umarci Pentagon da ta shirya daukar matakin soji a Najeriya, yana mai ikirarin cewa wannan shiri an yi shi ne don kare Kiristoci.
Sannan ya yi barazanar dakatar da duk wani tallafi ga kasar” idan gwamnatin Najeriya “ta ci gaba da yin biris ga kisan Kiristoci, Kalaman da suka haifar da fushi a fadin Najeriya.
Kungiyoyin fararen hula da masu sharhi kan siyasa sun zargi Trump da yada labaran karya da kuma haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma.
Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wadannan zarge-zargen da kakkausar murya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin da aka aikata a El-Fasher November 9, 2025 Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila November 9, 2025 An Kafa Mutum-mutumin Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran November 9, 2025 Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati November 9, 2025 Wasu Kasashe Takwas Sun Bukaci Ganin An kama Benjamine Netanyahu November 9, 2025 WFP: Ana Fama Da Matsananciyar Yunwa A Gabashin DRC November 9, 2025 Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro November 9, 2025 Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa November 9, 2025 Martanin Iran ya haddasa wa Isra’ila hasarar fiye da Dala Miliyan 200 November 9, 2025 Biden Ya Caccaki Trump Bisa Tuhumarsa Da Kawo Barna November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci