Leadership News Hausa:
2025-11-11@14:28:13 GMT

‘Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Kashe Ɗan Wasan Barau FC A Katsina

Published: 11th, November 2025 GMT

‘Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Kashe Ɗan Wasan Barau FC A Katsina

DSP Aliyu ya gargaɗi jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya, inda ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin aikata hakan za a hukunta shi.

Ya kuma roƙi mutane su dogara da sahihan bayanai daga hukumomi, tare da tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan ƙarƙashin CP Bello Shehu tana ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL November 9, 2025 Wasanni Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya November 9, 2025 Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana.

Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin nan kafin kowa ya ankara. Daga nan suka tsere da motarsu ba tare da sun cutar da wani ba.”

Wannan lamari ya jefa masu jefa ƙuri’a cikin firgici da tsoro, inda wasu suka bayyana damuwa kan abin da ka iya biyo baya kafin a kammala zaɓen.

Wani mazaunin yankin da ke wurin a lokacin faruwar lamarin ya ce: “Abin ya firgita mu. Ana zaune lafiya kawai sai a ji an kashe mutum haka. Wannan abu ya girgiza mu sosai domin ba a taɓa samun matsala irin wannan a  mazabar nan ba.”

Shi ma wani mai suna Odemenna, wanda ya kasance a wurin, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin gudanar da bincike da kuma neman waɗanda suka aikata wannan aika-aika.

A cewar wani mazaunin yankin, Chukwudi Chinanso: “Maharan sun kai harin ne kan kansilan, kuma sun yi sa’ar tarar da shi ne lokacin da ya zo jefa ƙuri’a. Da nan suka harbe shi suka gudu.”

Haka zalika, wata mata mai suna Joyce Okoro ta shaida cewa: “Wasu matasa ɗauke da muggan makamai sun zo mazabar mu suka harbe kansilan sannan suka tsere.”

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin rikicin siyasa ne ya haddasa kisan, kasancewar Nze Ala Kuru Orji ɗaya ne daga cikin shugabannin jam’iyyar APGA a mazabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’ansu sun shiga bincike domin cafke masu hannu a cikin wannan ɗanyen aiki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina
  • Xi Ya Halarci Bikin Bude Gasar Wasanni Ta Sin Karo Na 15 A Guangzhou
  • Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
  • Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15
  • Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya
  • ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra
  • Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato
  • Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko
  • Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya