Aminiya:
2025-11-10@15:16:05 GMT

An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP

Published: 10th, November 2025 GMT

Rahotanni na cewa rayukan mayaƙa 200 sun salwanta a sanadiyyar wani rikicin cikin gida tsakanin ’yan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne a yankin Dogon Chiku, kusa da Tafkin Chadi, a ranar Lahadi.

’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi

Bayanai sun ce wannan dai na daga cikin rigingimun da suka fi zafi tun bayan da ɓangarorin suka yi hannun riga saboda saɓanin ra’ayi a shekarar 2016.

Wani ɗan sa-kai da ke taimaka wa dakarun Nijeriya wajen sa ido kan lamurran tsaro, Babakura Kolo, ya ce sun ƙirga gawarwakin aƙalla mayaƙa 200.

“Mun ƙirga aƙalla gawarwaki 200, mafi yawansu na bangaren ISWAP,” in ji shi.

Shi ma wani tubabben ɗan Boko Haram mai suna Saddiku, wanda ke bin diddigin lamurran ƙungiyoyin, ya tabbatar da faruwar rikicin.

A cewarsa, “an kashe aƙalla ’yan ISWAP 200, kuma an ƙwace makamai da dama. Sai dai daga ɓangaren Boko Haram an rasa mayaƙa huɗu kacal.”

Majiyoyin tsaro ma sun tabbatar da aukuwar rikicin, inda cikin farin ciki wata majiyar sirri ta ce, “muna da bayanan da suka nuna an kashe mayaƙa fiye da 150, kuma wannan abu ne da ke rage musu ƙarfi.”

Tun bayan rabuwa tsakanin Boko Haram da ISWAP a shekara ta 2016, ɓangarorin biyu sun riƙa kai wa juna farmaki lokaci zuwa lokaci, musamman a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Jihar Borno.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano

Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale.

Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa

Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar.

“A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar da yaro ɗan shekara biyu, Danjuma Salman, wanda ya faɗa cikin wata rijiya da murfinta ya lalace,” in ji sanarwar.

Abdullahi, ya ce jami’an hukumar sun fito da yaron, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

An miƙa gawar yaron ga mahaifinsa, Salman Dayyabu, bayan an fito da shi daga rijiyar.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara na jihar, Alhaji Sani Anas, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen yaron.

Ya kuma yi kira ga mazauna unguwanni da su riƙa rufe rijiyoyi da sauran wuraren ruwa yadda ya kamata domin guje wa irin wannan iftila’i.

Haka kuma ya shawarci iyaye da su riƙa kula da yaransu sosai, musamman a wuraren da ke da hatsari.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5
  • Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno
  • Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
  • ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra
  • Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff
  • Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato
  • Ban ɓata zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff
  •  Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano