Za A Bude Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Koli Na 20 Na JKS A Watan Oktoban bana
Published: 30th, July 2025 GMT
Yau Laraba 30 ga wata, an kira taro a ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), inda aka yanke shawarar gudanar da cikakken zama na 4 na kwamitin koli na 20 na JKS a watan Oktoba na shekarar da muke ciki, domin nazari kan shawarar tsara shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15.
Taron ya nuna cewa, lokacin gudanar da “Shirin shekaru biyar-biyar din na 15”, lokaci ne mai muhimmanci a fannin tabbatar da ingantaccen tushe, da kokarin raya zamanantar da kasar Sin bisa tsarin gurguzu. A yanzu haka yanayin ci gaban kasar Sin yana fuskantar manyan sauye-sauye masu sarkakiya, akwai kuma damarmaki bisa manyan tsare-tsare da ma kalubale tare.
A waje guda kuma, tattalin arzikin kasar yana da tushe mai karko, da tarin fifiko, da karfin juriya, da kuma makoma mai kyau a nan gaba. Har ila yau, fifikon da kasar Sin ke da shi a fannonin tsarin gurguzu mai halin musamman irin na kasar, da kasuwa mai girma sosai, da cikakken tsarin masana’antu, da kuma albarkatun kwararru, ya fi bayyana sosai.
Taron ya kuma nuna cewa, kamata ya yi a kara azamar cimma nasara, da gudanar da ayyuka yadda ya kamata, don samun rinjaye bisa manyan tsare-tsare a yayin da Sin ke shiga takara a duniya, da ma samun babban ci gaba a ayyukan da suka shafi zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye.
Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.
“Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi.
Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rigaya ta tattara nata cikakken rahoton, wanda za a mika wa Gwamnan nan ba da daɗewa ba.
A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya nuna godiya ƙwarai ga Gwamnan Jihar bisa amincewa da baiwa kwamitin damar gudanar da wannan aiki mai muhimmanci.
Shugaban Hukumar gudanarwa na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana godiya ga Sarkin Karaye bisa sadaukarwa da haɗin kai da ya bayar, wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin kwamitin.
Abdullahi Jalaluddeen