Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita
Published: 11th, November 2025 GMT
Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita.
Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu sama da 620, wanda hakan ya zama keta dukkan ka’idoji da kudurori na kasa da kasa da aka amince da su.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna Allah wadai da karya wannan yarjejeniya da aka yi akai-akai kuma muna daukar ‘yan mamayar da alhakin sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro da na jin kai.
Muna jaddada cewa ci gaba da wannan lamari yana barazana ga yarjejeniyar da kuma kasashen da ke da alhakin aiwatar da ita.”
Tun bayan soma yakin Gaza a watan Oktonan 2023 jimillar wadanda sukayi shahada a Gaza ya kai 69,179, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 170,693, a cewar sabbin alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci November 11, 2025 Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Guda Uku Zuwa Sararin Samaniya November 11, 2025 Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10 November 11, 2025 An Sake Bude Gidajen Mai Da Makarantu Da Aka Rufe A Kasar Mali November 11, 2025 Trump Ya Yi Wa Ma’aikatan Filayen Jiragen Sama Barazana November 11, 2025 Donald Trump Na Amurka Ya Karbi Bakuncin Shugaban Rikon Kwaryar Kasar Syria Ahmad Shar November 11, 2025 Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kamaru: Jagoran ‘yan Hamayya Chiroma Ya Bai Wa Gwamnati Sa’o’i 48 Da Ta Saki Dukkanin Wadanda Aka Kama Bayan Tsabe
Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.”
Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira ” Nuna wariya ta kabilanci.”
Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.”
A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%.
Shi dai Chiroma ya bayyana cewa shi ne wanda ya lashe zaben, illa iyaka mahukuntan kasar sun yi magudi ne da sauya alkaluman kuri’un da aka kada.
Wani rahoto na MDD ya ce; Jami’an tsaron kasar Kamaru sun kashe masu Zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben 48, yayin da mahukuntan kasar suke cewa mutane 5 ne su ka rasa rayukansu.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban kasa, inda ya yi kira da a kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake yi.
A karshen sakon nasa, Chiroma ya ce idan har ba a yi aiki da bukatar da ya bijiro da ita ba, to kuwa mutanen kasar za su yi duk abinda za su iya domin kwato da ‘ya’yansu da ake tsare da su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Jarida 44 Ne Su Ka Yi Shahada A Sansanonin Hijira Na Gaza November 10, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Isra’ila” A Yankin Saida November 10, 2025 Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali November 10, 2025 An Fara Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Sheikha Hind Bint Maktoum November 10, 2025 Zaben Iraki: Gwaji don ‘yancin siyasa da kawo karshen tsoma bakin Amurka November 10, 2025 Iran da Rasha sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa November 10, 2025 Iran ta nuna damuwa kan zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan November 10, 2025 Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa November 10, 2025 Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean November 10, 2025 Lebanon: Mutane 28 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila tun daga watan da ya gabata November 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci