Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin
Published: 11th, November 2025 GMT
Zhang Lei, mataimakiyar shugaban sashen yada labaru na kamfanin BaySystems reshen Sin da yankin arewa maso gabashin Asiya, ta kara da cewa, “A cikin shekaru 140 da suka gabata, mu kasance a nan ba mu taba barin ba, ko a lokacin wahala ko a’a. Wannan yana nuna irin kauna da alkawarin da wannan tsohon kamfanin Jamus mai shekaru 100 ke da su ga kasar Sin.
A game da hakan, Frank Hammes, babban darektan kamfanin IQAir na kasar Switzerland ya bayyana cewa, bikin CIIE tamkar dakin gwaje-gwaje ne a gare mu, inda ban da baje kolin sabbin nasarorinmu, muna kuma iya samun martani daga masu sayayya.
Shi kuma Mr. Yu Feng, babban darektan kamfanin Honeywell da ke kula da harkokin kasar Sin, ya ce, masu sayayya wadanda da wuya a biya bukatunsu, alheri ne ga kamfanonin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, sabo da su ne suke taimakawa wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani.
“Za mu ci gaba da zuba jari a Sin har na karni 1”, “Za mu kara kusan shaguna 100 a Sin”. Nicolas Hieronimus shugaban kamfanin L’Oréal da Sandeep Seth, babban ma’aikacin kamfanin Tapestry sun fadi hakan yayin zantawar da wakilin CMG ya yi musu.
Hieronimus ya ce, “Sin ita ce kasuwa ta biyu mafi girma a duniya gare mu, kuma cibiyar kirkira ce mai karfi.” Seth kuma ya ce, “Kasuwar Sin ta zama filin gwajin sabbin dabaru.”
Wadannan kalamai sun nuna yadda suke amincewa da CIIE, tare da bayyana niyyar su ta ci gaba da fadada kasuwancinsu a Sin. (Lubabatu Lei da Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Halarci Bikin Bude Gasar Wasanni Ta Sin Karo Na 15 A Guangzhou
Gasar ta kasa ita ce irinta mafi girma da ta kunshi wasanni daban-daban, kuma an fara ta ne a shekarar 1959. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA