2025-05-06@23:49:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 535
«Yan gudun hijira»:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin...
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki...
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin...
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani...
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana...

Fira Ministan Indiya Ya Bayyana Cewa: Iran Tana Kokari A Fagen Inganta Zaman Lafiya A Yanki Da Duniya Baki Daya
Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya...

Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba
A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba! Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a...
Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa. A jawabinsa yayin taron, Gwamna...

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga...
A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a Arewacin Sudan sun kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu, haka nan kuma sun yi sanadiyyar yanke wutar lantarki a yankin. Kafar watsa labaru ta “al-muhakkak” ta ce; Dakarun...
Francis, wanda aka zaba a matsayin gwarzon Shekarar na TIME a 2013, ya zama Fafaroma na farko na da ya fiton daga yankin Latin Amurka lokacin da ya karbi ragamar cibiyar addinin. A cikin wa’adinsa, Francis ya ya yi suna wajen tawali’u da kiran zaman lafiya yayin da duniya ke fuskantar manyan kalubale, da suka...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya bayyanawa firai ministocin kasashen Indiya da Pakistan a maganar da yayi da su ta wayar tarho a jiya Asabar, kan cewa mu hada kai gaba daya don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkiya yana fadawa shuwagabannin kasashen biyu, kan...
Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar...

Tashin Gobara A Tashar Jirgi Ruwa Na Shahid Raja’i Da Ke Kudancin Iran Ya Lashe Rayukan Mutane A Kudancin Iran
Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar...

‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan
‘Yan gudun hijira a Sudan sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su ceto yara da tsofaffi daga mummunan kangin da suka shiga An gwabza kazamin fada a kusa da birnin El Fasher da ke arewacin Darfur tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka yi ruwan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Karo na hudu kenan da Arsenal ta kara da Real a kofin Zakarun Turai, inda ta ci uku aka yi canjaras daya. A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karbi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako daya bayan haka. Kungiyar dai ita ce a mataki na biyu a...
Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude. Jaridar Middle eart...

Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ke Ci Gaba Da Rike Kambun Kasa Na Mafi Yawan Samar Da Danyen Mai A Afirka — OPEC
A cewar kungiyar ta OPEC, wannan ya ya faru ne duk da raguwar yawan man da Nijeriya ta samar a watan da ya gabata, musamman idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairun da ya gabata. Rahoton ya ci gaba da cewa, duk da raguwar, yawan Man da kasar...
“Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho. Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA...
Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama. Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da...
A watan Janairu kawai, marigayi shugaban ‘yan fashin daji, Isuhu Yellow, ya sanya harajin naira miliyan 172.7 a kauyuka 25, ciki har da bukatar amfanin gona. A misali, an kakaba wa kauyen Gijinzama harajin naira miliyan 8.5, Dakolo naira miliyan 5 da buhunan wake 20, da Kibari, Kunchin Kalgo naira miliyan 20, Sungawa naira...

Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a yau domin gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa: A yau ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a karkashin jagorancin tawagar diflomasiyya...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan...
Shugaban Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan Isra’ila Netanyahu ba zai ja shi zuwa shiga cikin yaki da Iran ba, kuma a shirye yake ya gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci da shugaban kasar Iran Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya jaddada cewa: Ba za a sanya shi shiga yaki da Iran ba saboda...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta inganta fahimtar juna tsakanin Indiya da Pakistan Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya sanar a yau Juma’a cewa: kasarsa a shirye take ta yi aiki mai kyau a fagen sulhunta tsakanin Indiya da Pakistan don inganta fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu...
“Saboda ragin farashin litar man fetur da Dangote ya yi ne. Gidan man yana da tsohon mai da ya saya a farashin da ya fi wannan, kuma ba zai sayar da shi a asara ba. “Wannan dalilin ne ya sanya muka rufe gidajen man tun ranar Talata. Da yiwuwar mu bude nan gaba.” ...

Sojonin Yemen Ta Kakkabo Jiragen Yakin Amurka Wadanda Kimarsu Ya Dalar Amurka Miliyon $200 A Makonni 6
Sojojin kasar ayemen sun kakkabo jiragen yaki na kasar Amurka wadanda ake sarrafashi daga nesa a kan kasar Yemen, da dama wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon $200 a cikin makonni 6 kacal. Tashar talabijin ta Pressstv a nan Tehran ya bayyana cewa wadan nan jiragi suna aikin leken asiri ne a kan kasar...
A cikin sabban hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Alhamis sun kai hare-hare kan larduna guda 4 . Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ta nakalto majiyar labarai daga kasar ta Yemen jiragen yakin Amurka suna kai hare-haren a kan kasar kusan ko wani rana. Amurka dai tace tana...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gbaata wadanda suka shafi siyasa, tsaro tattalin arziki zamantakewa da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da...
“Aisha ba wai mawaƙiyar amshi ba ce kawai a wajen Rarara ba. Sun yi matuƙar shaƙuwa da juna, kuma mu da muka san su ba abin mamaki ba ne don an ce za a yi wannan aure,” in ji majiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
’Yan bindiga sun kashe wani sabon ango, sun kuma yi wani gaba da amaryasa bayan kwanaki 11 da ɗaura aurensu a wata unguwa a Jihar Nasarawa. Ganau sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai hari gidan sabbin ma’auratan ne da misalin ƙarfe karfe 11:00 na dare ranar Laraba, inda suka harbe angon har...
Kafafen watsa labarun HKi sun amabci cewa daya daga cikin sojojinsu ya halaka a Gaza, yayin da wasu 7 su ka jikkata. Kafafen watsa labarun na HKI sun ce, Harin da aka kai wa sojojin ya kunshi harbi daga kwararren maharbi da kuma harba makamin dake fasa motoci masu sulke. An ga jiragen sojan mamaya...

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma...

Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya
Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a...

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa. Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2...
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya. Yayin ganawarsa da...
Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga...
Matsalar tsaro ta kara tabarbare a jihohin Filato da Benuwai, inda rahotanni ke cewa, wasu da ake zargin makiyaya ne daga kasashen waje ne ke kai hare-haren kashe rayuka da kuma raba al’umma da matsugunansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da...

Al’ummar Gaza Suna Tsananin bukatar Agaji Da Kiran A Tilastawa Gwamnatin Mamayar Isra’ila Bude Mashigar Yankin
Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata...
Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana...

Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka...
Ya roƙi matasa da su zauna lafiya kuma su riƙa kai rahoton duk wani abu na barazana ga jami’an tsaro, domin nemo mafita game da hare-haren da ke ci gaba da faruwa. Garba Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da makiyayan shida ke kiwo. “Da maharan suka fara harbi, ɗaya daga cikin...
‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa. Mahalarta taron sun yi kira ga...