Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ta Amince Da Bukatar Kawo Karshen Rikicin Jin Kai Cikin Gaggawa A Gaza
Published: 30th, January 2025 GMT
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa
Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15.
Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai.
A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda 18 suka nuna adawarsu da kudurin, yayin da wakilai 14 suka ki kada kuri’a.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamatin Tantance Ayyukan Kananan Hukumomi Na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Isa Sule Tankarkar
Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su.
Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan tsokaci ne a sakatariyar karamar hukumar Sule Tankarkar a ci gaba da rangadin kananan hukumomi da kwamatin yake yi.
A cewar sa, kwamatin zai tantance kasafin kudin karamar hukumar na shekarar 2024 da 2025 na ayyuka ta da jerin ayyukan raya kasa, da takardun biyan kudaden ayyukan da littafin ta’ammalin kudaden na banki.
Yace kwamitin zai tantance takardun kudaden shiga tare da duba kudin tarukan bangaren zartaswa da na kansiloli domin tabbatar da bin ka’idojin kashe kudaden gwamnati.
Karamin kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashim Kanya ya duba aikin masallacin kamsissalawati na Rugar Danqulili, da famfunan tuka tuka a Gabala/Dangwanki da Yanyawai da Fulanin Tagai da Rugar Hardo Daudu da gidan ungozoma a asibitin Jeke, da shirin noman rani a Maitsamiya.
Kazalika, kwamati na biyu bisa jagorancin wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari ya duba aikin gidan ruwa mai amfani da hasken rana a unguwar Sule Gabas da masallacin Juma’a na Hammado da makarantar Tsangaya a Danladi, da masallaci kamsissalawati na gidan mulki na Shugaban karamar hukumar da famfon tuka tuka na Gidan Idi Ruwa.
A nasa Jawabin, Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar Malam Tasi’u Adamu, Ya lura cewar, tantance sha’anin mulki da harkokin kudin kananan hukumomi ko shakka babu zai taimaka wajen kawo ci gaban yankunan karkara.
Malam Tasi’u Adamu ya kuma yi addu’ar samun nasarar ziyarar kwamatin domin ta yi tasiri wajen kawo cigaban rayuwar jama’ar yankin.
Usman Mohammed Zaria