Kungiyar Tarayyar Turai ta yi barazanar sake kakaba wa Syria takunkumi
Published: 12th, March 2025 GMT
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria.
Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.
Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas : Isra’ila ta yi amfani da sulhu wajen tattara bayanai kan shugabannin Hamas domin kashe su
Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da sulhun da aka cimma wajen tattara bayanai kan shugabannin kungiyar ta bi tana kashe su.
Saidai mai magana da yawun kungiyar ya ce kungiyar tana da tushe sosai a Falasdinu wanda kisan gillar da Isra’ila ke yi wa shugabanninta ba, bai zai rusa ta ba.
Sami Abu Zuhri ya bayyana hakan ne bayan da Isra’ila ta kashe wasu jami’an ofishin siyasa na kungiyar ta Hamas guda hudu cikin kasa da mako guda tun bayan da ta koma yakin kisan kare dangi a zirin Gaza, wanda hakan ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyu da Hamas.
Jinin shugabanni da kwamandojin Hamas iri daya ne da na yara da matasa na Gaza, kuma wadannan kashe-kashen ba za su hana mu ci gaba da gwagwarmaya ba.
Kakakin na Hamas ya kuma nuna rashin jin dadin yadda Isra’ila ke aiwatar da hukuncin kisa a kullum a yankin da aka yi wa kawanya.
“Abin da ke faruwa a Gaza a yanzu ya fi yakin kisan kare dangi da aka shafe watanni 15 ana yi,” in ji shi.
Rahotanni na baya-bayan nan na cewa, akalla Falasdinawa 23 da suka hada da kananan yara bakwai ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai da kafin wayewar gari a wannan Talata.