2025-10-13@22:24:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 548

«Ya yi bayanin»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen. jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.
    Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu cewa a Facebook ya haɗu da ita, inda daga bisani ta ziyarci ɗakinsa a unguwar Olunlade a garin Ilori, bayan ta je wani biki. Sai dai ya musanta zargin da ake masa na kashe ɗalibar mai suna Hafsah Yetunde Bello domin yin tsafi. Jirgin soji ya kashe fararen hula a Katsina Malaman addini sun yi wa ’yan siyasa juyin mulki —Sule Lamiɗo Ku tona asirin...
    Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta. Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan. Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin Jordan fiye da wadanda Falasdinawa suke ginawa. Wannan dai shi ne lokacin farko da HKI ta dawo da siyasar rusau a yammacin kogin Jordan tun a 1967. Wannan matakin na HKI yana zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Robio yake ziyara a Tel Aviv, kuma a lokacin da Amurkan ta bai wa HKI bama-baman MK-84 har guda 1,800.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka a yanzu? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan.
    Wata majiya daga CBN ta bayyana cewa idan ba tare da cikakken tantance kudi ba, babban bankin ba zai iya bude sabbin asusu ga kananan hukumomin ba.
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya  kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai. A wata hira da tashar talabijin ta  “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya ce, ya na son Amurka ta mallaki ma’anadai na kasar  Ukiraniya a matsayin ladar da tallafin sojen da take bukata daga Amurka. Gwamnatin Donald Trump ta gabatar wa da Kiev shawarar yin musayar ma’adanai na musamman da irinsu sun yi karanci a duniya, da take da su, na kaso 50%  da hakan zai zama abinda take biyan Amurka da su, madadin taimakon soje...
    Babban sakataren MDD Antonio Guterres  wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji. Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake bukatuwa da su, domin taimakawa mutanen kasar ta Sudan da yaki ya daidaita. Babban magatakardar MDD ya yi ishara da rawa ta jarunta da kungiyoyin mata  suke yi a cikin yanayi mai hatsari,tare dayin kira da a kare rayukan fararen hula. Har’ila yau ya yi kira da a kawo karshen shigar da makamai zuwa kasar ta Sudan da bai wa zaman lafiya dama, a cikin...
    kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani musayar fursunonin da aka sako Falasdinawa 369 a wata musanya ta baya-bayan nan a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. An saki ‘yan Isra’ilan uku a birnin Khan Yunus da ke kudancin Gaza, inda Isra’ilawan suka yi jawabi ga jama’a kafin mika su ga kungiyar agaji ta Red Cross. Sakin dai shi ne na shida tun bayan da tsagaitawar ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu bayan fargabar da ake yi a makon da ya gabata cewa yarjejeniyar ta kusa rugujewa bayan da Isra’ila ta ki ba da isassun kayan agaji a Gaza. Yawancinsu...
    A nasa jawabin, Jatau ya bayyana cewa, duk da cewa kisan da aka yi wa wani malamin addini lamari ne mai ban tausayi, amma babu wata kwakkwarar shaida da ke alakanta lamarin da wata kungiya, addini ko kabilanci. Ya tuna irin abubuwan da suka faru a baya inda daga baya aka gano wadanda suka aikata laifin ‘yan kungiya daya ne ko kabila ko addini. Jatau ya kuma umarci jami’an tsaro da su kama wadanda ke da hannu a kisan tare da tabbatar da an hukunta su. Ya bukaci shugabanni da su kasance masu kamun kai da hakuri wajen tafiyar da irin wadannan al’amura masu muhimmanci domin hana faruwar lamarin. “Ina kira gare ku a matsayinku na shugabanni da ku yi...
    A yau Asabar ne aka bude taron shugabannin kasashe da gwamnatocin AU a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na Habasha. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...
    A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli.   “A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.”   Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron COP29 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na...
    Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa. Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano Haruna Zago ya kasance Shugaban Hukumar REMASAB tun ranar 5 ga watan Yuli, 2023, bayan naɗin da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi masa.
    An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda...
    An gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna kan yi wa wata matar aure da mijinta dukan kawo wuƙa a yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano. An gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gazawa kan zargin yi wa matar auren karaya uku a ƙafarta da hannunta bayan sun yi mata dukan kawo wuƙa tare da ji mata raunuka. Sun kuma ƙuƙƙuje mijinta da ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan shi ma suka lakaɗa masa duka. Ana tuhumar su laifin yin kutse da yin barazana da haɗa kai wajen aikata laifi da ji wa mutane munanan raunuka. ’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba Ɗan fashi ya yi...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, wanda zai yi magana a kan “Yadda JMI Ta Bunkasa Sana’argine-gine da da kamfanoni tare da amfani da fasahar cikin gida’ wanda ni tahir amin zan karanta. Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979, daya daga cikin bangarorin da aka sami gagarumin ci gaba a cikinsa shi ne, bunkasa sana’ar gine –gine da kuma samar da masana’antu, wanda ya kai ga kasar ta kai ga wadata a wannan bangaren, wani abu daga kasashen waje, sai abunda ba za’a rasaba. Har’ila yau wannan ya wadanar da mutane da dama a kasar. Kafin haka idan mun dubi...
    Sojojin Sudan suna kokarin canza ma’aunin yaƙin kasar bayan da suka sun tunkari birnin Khartoum fadar mulkin kasar domin yantar da shi gaba daya Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya kara kamari a ‘yan kwanakin da suka gabata. Sojoji suna kara ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan fitattun sojojin kasar da suka hada da sojoji da mayaka masu goyon bayan sojoji da hukumar leken asiri da dakarun tsaron Sudan da suke sansanin Haddab da ke bangaren arewa maso gabashin yankin Gabashin Nilu a arewa maso gabashin Khartoum suka doshi birnin na Khartoum da...
    Manchester City ta tsallake rijiya da baya a gidan Orient, bayan ta doke su da ci 2-1, hakan ya sa ta tsallaka zuwa zagaye na biyar na gasar cin kofin FA ranar Asabar. Kamar kullum, Kevin De Bruyne ne ya fitar da kitse daga wuta ana gab-da za a tashi daga wasan. Mai tsaron ragar Manchester City, Stefan Ortega ne ya ci gida tun a minti na 16 da fara wasan, sabon dan wasan City Khusanov ne ya ci kwallonsa ta farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kafin Kevin De Bruyne ya jefa ta biyu. Mutanen Guardiola kuwa su na matsayi na hudu a gasar Firimiya, hakazalika za su hadu da zakarun Turai, Real Madrid a gasar zakarun Turai...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshiyan ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata jada baya ba, kuma ba zati yi  rauni ba saboda takunkuman zaluncin da kasashen yamma suka dorawa kasar. Ya ce kasar tana da arzikin da zata ci gaba da kasancewa a gaba da kasashen da dama a yankin Asiya ta kudu, duk tare da wadannan takunkuman. Tashar talabijin ta Press tv ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a garin Sirjan, daga  na kudu masu gabacin lardin Kerman. Inda ya gabatar da kamfanoni da ayyukan jama’a wadanda aka kammala, wadanda suka hada har da sabbin wuraren yawon bude ido da kuma shakatawa. Shugaban y ace, kasar Iran ba zata jada baya ba, sannan makiyan kasar sun...
    A bayan nan ne mahukunta a Ƙaramar Hukumar Agege, a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙaramar Hukumar Agege, Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi suka kulle babban masallacin Hausawa na garin, biyo bayan wani rikici da ke da alaƙa da na limanci ya ɓarke a masallacin a ranar Juma’a makon jiya. Rikicin na zuwa ne bayan rasuwar babban limamin garin Agege, Shaikh Sharif Habib Abdul-Majid, wanda ya rasu kwanaki biyu gabanin aukuwar lamarin. Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2 An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na zamani, an ga masallata a cikin masallacin suna kai wa junansu duka, wadanda suka haɗar da ɓangarori uku. Waɗanda suka bai wa...
    Kazalka, matsalar ta sanya wasu iyalai da dalibai da dama a kasar yin kokarin jurewa matsin rayuwar da suke ci gaba da fuskanta, wanda hakan yak e kuma kara zamowa, babbar barazana ga rayuwarsu. Bisa fashin baki da rahoton ya yi ya nuna cewa, a shiyoyi shida na kasar, banbancin hauhawan farashin na kayan abincin, ya sha ban ban, inda a yakin Kudu Maso Yamma, lamarin na hauhawan farashin kayan abincin, ya fi yin kamari.
    An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa  tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano. ’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya, kasancewar mahaifiyarsa da mahaifin sun rabu. Bayanai sun nuna cewa duk da cewa kakar ta ki amincewa, amma sai da matar ta nace ta dauki yaron da cewa za ta kula da shi, bayan nan ne kuma sanya masa tafasasshen ruwa a gaban nasa, maimakon ruwan dumi. Duk da raunin da tafasasshen ruwan ya yi  masa kuma, sai aka kai shi wurin mai maganin gargajiya...
    Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan shekarar ta 2025, inda ta buga wasanni da dama ba tare da tayi rashin nasara ba tun bayan shigowar sabuwar shekara, kuma daya daga cikin mafi kyawun sakamakon da ta samu ya zuwa yanzu a bana shi ne wanda ta doke Valencia da ci 7-1 kwanaki 10 da suka gabata. Har Yanzu Arsenal Ta Na Iya Lashe Gasar Firimiya Ta Bana – Alan Shearer Ba...
    Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan  ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa;  A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara bayyana, don haka wajibi ne jami’anta su fuskanci shari’a akan kowane rai daya da aka yi asararsa. Cobyn ya ci gaba da cewa; Duk wanda ma ya rika aikewa da makamai yana sane da cewa za a yi amfani da su a yi kisan kiyashi, shi ma a hukunta shi.” A cikin watanni shida da su ka gabata Birtaniya ta sayar wa da HKI makamai...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf a wani taron manema labarai da ya yi da takwaransa na Iraki Mahmoud al-Mashhadani, ya bayyana cewa: Kasashen Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare gwagwarmaya, yana mai jaddada cewa: Iran da kawarta Iraki sun kuduri aniyar marawa bangaren gwagwarmaya baya domin kare Musulunci da martabar al’ummar musulmi. Baqir Qalibaf ya kara da cewa: Sun ba da muhimmanci wajen raya hanyar layin dogo, musamman sabuwar...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara da cewa zai dorawa hatta kayakin da suke shigowa Amurka daga kasashen Turai, nan gaba, sai dai bai sanya lokaci ba. Kafin haka dai shugaban ya bayyana cewa zai dorawa kasar Canada kashi 25% kan dukkan kayakin da suke shigowa kasar. Sai mna Desel, inda zai sanya kashi 10% kacal.
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta. Daga watan Disamban 2024 da Hisbah ta yi sanarwar zuwa yanzu, an samu ɓullar aƙalla bidiyoyi 10 daga jihar da suka tayar da kura a kafofin sada zumunta, musamman TikTok, ciki har da na tsiraici. Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara Ɓullar bidiyon tsiraicin fitattun ’yan Tiktok irin su Hafsat Babaiana da Hafsat...
      Kayan hadi: ”Yayan Hulba (gongoni 2, Aya (gongoni 3), Ridi (gongoni 1)   Ga kuma Yadda za ku hada: Wadannan kayan hadin ku soya su duka amma sama-sama sai ku bar su su huce sanna ku daka ko ku nika ku tankade.   Yadda ake amfani da ita: Za ku dinga diban cokali 2 ko 3 kusa madara cokali 2 kusa ruwan zafi ku gauraya ku shanye, sannan ana sha ne safe da rana da dare na tsawon sati 3 ko 4. Kazalika ku nemi garin hulba ku debi kadan kusa ruwan zafi ku gauraya sai ku sanya wani abu ku dinga dandanar ruwan kuna gasa shi, sannan ku samu man hulba da man zaitun da man ridi ku...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
    Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne. Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda zasu nunasu nan ba da dadewa ba. Sannan ya kara da cewa dukkan jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aiki na zama, wanda sabbin jiragen saman yakin da ake kerasu a wasu kasashen basu yi gaba da su a wani daga cikin a kayakin aiki na zamani ba. Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Tasnim wanda ya nakalto babban kwamnadan...
    Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai samame a wasu gidajen jama’a a birnin, inda suka kama wasu da ake zargin ɓarayi ne tare da ƙwato kayayyakin da aka sace. Wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da: naɗin igiyoyin wutar lantarki masu yawa, an baje kolin su a yayin da rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta gabatar waɗanda ake zargin a ranar Juma’a Ga wasu hotunan kayan da aka ƙwato:          
    ’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. ’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa  da Birnin Yero. A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu tara, ciki har da mata hudu. Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haifar da fargaba. Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa A kauyen Birnin Yero, ’yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a lokacin...
    A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza.  Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
    Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo na ‘Afirca News’ ya nakalto kagami yana cewa ya a shirye yake ya shiga yaki da kowa saboda kare matsayinsa. A yau Alhamis dai mayakan M23 sun kammala kwace iko da birnin Goma babban birnin yankina kuma a halin yanzu sun nosa zuwa garin Bukavu babban birnin lardin Kivu ta kudu. Wannan dai shi yaki mafi girma wadanda ake yi a yankin KIvi tun shekara...
    Shugaba Felix Tsisekedi na Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ya bukaci hadin kai na al’ummar kasar tare da sanar da mayar da martini kan rikicin gabashin kasar dake da nasaba da kungiyar ‘yan tawaye ta M23. A yayin wani jawabi ga al’ummar kasar, shugaban na Kongo ya yi kira da a hada kai tare da ba da tabbacin cewa “ana ci gaba da mayar da martini kuma an karfafa tsarin tsaro. ” Ya kuma yi tir da gazawar kasashen duniya da kasancewar dubban sojojin Rwanda a kasar tare da bayyana kungiyar ta M23. Wannan dai shi ne karon farko da shugaban na Kwango ke magana tun bayan harin da ‘yan tawayen suka kai a gabashin kasar a garin Goma. Yayin jawabin shugaban...
    Wani jami’in fadar mulkin Amurka ( White Hosue) ya nakalto shugaban kasar Amurka Donald Trump yana fada a yau Laraba cewa, shugaban kasar Amurkan ya rattaba hannu akan wata doka ta fada da kin jinin yahudawa da ta kunshi cewa duk wasu dalibai ‘yan kasashen waje da masu ci rani a kasar,  idan su ka shiga cikin Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa to za a kore su daga Amurka. Dokar da Trump din yta sanya hannu a kanta ta kuma kunshi bayar da umarni da ma’aikatar shari’ar kasar aka cewa ta bi diddigin duk masu barazanar ta’addanci, da ruruta wutarsa, da mabarnata dake cutar da yahduawan Amurka.” Haka nan Trump ya ce zai soke izinin shiga cikin kasar ta Amurka...
    Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake  gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki. Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba. Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin. A ranar Litinin din da ta gabata...
    Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
    Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC. Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi ƙarin haske dangane da barazanar harin ’yan ta’adda da ta yi gargaɗin aukuwarsa a bayan nan. Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun ɗauki matakan da suka dace biyo bayan barazanar harin ’yan ta’adda musamman a yayin taron Maulidin Shehu Ibrahim Inyass na ƙasa da aka gudanar ranar Asabar a jihar. Ɗan shekara 30 ya mutu a kududdufi a Kano ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike “Mun ankarar da jama’a sannan muka ɗauki matakan da suka dace domin tunkarar lamarin,” in ji CP Garba. Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin dangane da lamarin...
    Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta. Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu. SERAP ta maka Tinubu da NCC a kotu kan kara kudin kiran waya da data Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai. Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan...
    Mutane Na Yawan Tambaya Ta Yaushe Zan Yi Aure – Firdausi Yahaya