Kasancewar “Taiwan A Matsayin Lardin Kasar Sin” Shi Ne Matsayin MDD A Ko Yaushe
Published: 10th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”.
Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin MDD a ko yaushe kuma haka abun yake a tarihi.
Mao Ning ta jaddada cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana bin ka’idar kasancewar Sin daya tak, da kuma ra’ayi daya da aka samu na shekarar 1992, kana tana matukar son yin kokari don ganin an samu damar dinkuwar kasar Sin cikin lumana da gaskiya da sa himma. A sa’i daya kuma, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare ikon mallakar kasarta da cikakken ‘yancin yankinta, da kuma fitowa da kakkausan harshe wajen nuna adawa da ayyukan ‘yan aware na neman ‘yancin kai na Taiwan da tsoma baki daga waje. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Yace Huldar kasar Iran Da IAEA Zai Ci Gaba Ne Idan Ta Daina Fuska Biyu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu kai tsaye ko kuma ta yi amfani da wakilanta a cikin Iran don yin wannan aikin.
Banda haka Hukumar ta rufe idanunta kan shirin makaman Nukliya na HKI gaba daya. Daga karshe yace Iran zata sauya yadda take hulda da hukumar a lokaci guda tana bin hanyar diblomasiyya don warware matsalolin da suke rage tsakaninta na hukumar.