Wasu ‘Yan Bindiga Sun Bindige Fasto A Gombe
Published: 15th, February 2025 GMT
A nasa jawabin, Jatau ya bayyana cewa, duk da cewa kisan da aka yi wa wani malamin addini lamari ne mai ban tausayi, amma babu wata kwakkwarar shaida da ke alakanta lamarin da wata kungiya, addini ko kabilanci.
Ya tuna irin abubuwan da suka faru a baya inda daga baya aka gano wadanda suka aikata laifin ‘yan kungiya daya ne ko kabila ko addini.
Jatau ya kuma umarci jami’an tsaro da su kama wadanda ke da hannu a kisan tare da tabbatar da an hukunta su. Ya bukaci shugabanni da su kasance masu kamun kai da hakuri wajen tafiyar da irin wadannan al’amura masu muhimmanci domin hana faruwar lamarin.
“Ina kira gare ku a matsayinku na shugabanni da ku yi hakuri, ku kwantar da hankalin ku, ku yi tsayin daka har sai an kama masu laifin. Za ku iya tunawa a wani lokaci da ya wuce lokacin da aka kashe wani Fasto kuma daga baya aka gano cewa masu laifin ’yan coci daya ne. Kwanan nan an samu kashe-kashe a garin Kuri da ke karamar Hukumar Yamaltu-Deba kuma abin da ake magana a kai shi ne Fulani makiyaya ne amma daga baya aka gano cewa ba Fulani ne masu laifin ta kowace hanya ba,” in ji shi.
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Nijeriya, Rabaran Joseph Alphonsus Shinga, tare da shugaban ECWA reshen arewa maso gabas, Reberend Isa Uba, da shugaban DCC na Gombe, Reb Dr Adamu Dauda, sun kuma jajantawa al’ummar Kirista da su kalli lamarin a matsayin wani bangare na kalubalen da masu bi ke fuskanta. Sun jadadda cewa irin wadannan bala’o’i suna tunatar da bukatar dogara ga shirin Allah.
Shugaban kungiyar ta CAN ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin jihar ta nuna bakin cikin su kuma ta himmatu wajen ganin an kamo masu laifin. Shugaban hukumar ta DCC ya nuna jin dadinsa ga yadda gwamnati da jami’an tsaro suka dauki matakin gaggawa bayan faruwar wannan mummunan lamari.
কীওয়ার্ড: Ƴan Bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
“Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.
“Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.
“Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da wani asusu, a Zamfara a shirye muke mu ba da tallafin, idan kun shirya gobe, mu ma mun shirya.
“Mun shirya, kuma ƙofar mu a buɗe take, duk wani abu da zai kawo sauyi mai kyau a Zamfara muna maraba da shi, muna buƙatar tsari na abin da ku ke yi domin mu ci gaba da bin diddigin lamarin, zan samu wata tawaga da za ta riƙa hulɗa da cibiyar yaƙi da ta’addanci.
Tun da farko, Shugabar Rigakafi da Yaƙi da Ta’addanci (PCVE), Ambasada Mairo Musa Abbas ta ce, tawagar ta zo jihar Zamfara ne a madadin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da kuma kodinetan yaƙi da ta’addanci na ƙasa, Manjo Janar Adamu Garba Laka. “Muna nan a matsayin wani bangare na dabarun bayar da shawarwari na ƙasa baki ɗaya.”
“Muna son sake gode muku bisa irin karramawar da ka yi mana a Jihar Zamfara da kuma irin shugabancin da ka yi wa al’umma, muna sa ran haɗin kai don ganin cewa Zamfara ta zama kan gaba wajen yaƙi da ‘yan bindiga.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp