Amurka : Trump Ya Katse Tallafin Jami’ar Columbia, Saboda Zanga-zangar Goyon Bayan Falasdinu
Published: 9th, March 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump, ya katse tallafin da yake baiwa jami’ar Columbia saboda zanga-zangar goyan bayan Falasdinu.
Trump ya ce an katse tallafin na dala miliyan 400 ga jami’ar, daya daga cikin manyan a kasar, bisa zarginta da gazawa wajen fuskantar ayyukan kyamar Yahudawa a harabarta, wanda ke nufin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
Ana kallon wannan a matsayin alwashin da Donald Trump, ya sha a lokacin yakin neman zabe inda sha yin tir da yadda wasu jami’o’i ke nuna gazawa wajen fuskantar zanga zangar goyan bayan Falasdinu.
Masana da dama na ganin matakin a matsayin misali na siyasantar da manyan makarantu da kuma tsoma bakin gwamnati.
Shugaban kungiyar jami’o’in Amurka ya bayyana cewa matakin na gwamnatin Trump “ya haifar da matukar damuwa game da sha’anin ilimi da kundin tsarin mulkin Amurka kan ‘yancin fadin albarkacin baki.
Dama Trump ya sake nanata barazanarsa a wannan makon, inda ya yi alkawarin rage kudaden da ake ba duk jami’ar da ta ba da damar gudanar da zanga-zanga ba bisa ka’ida ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Nathaniel Terwanger Kumashe a ƙauyensa da ke ƙaramar hukumar Tarka a Jihar Benuwe.
An samu rahoton cewa wanda aka yi garkuwan ya taso ne daga Makurdi sansaninsa, domin halartar jana’izar ɗan uwansa da ya rasu a lokacin da aka ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.
Nasiru Ahali Shahararren masanin masana’antu a Kano ya rasu Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDPWani kawun wanda aka yi garkuwan, tsohon mai baiwa gwamnan Jihar Benuwe shawara kan harkokin sufuri, Cif Yimam Aboh, ya shaidawa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an ɗauke jami’in, Insfekta Kumashe a daren Laraba da misalin ƙarfe 10 na dare.
Ya ce, ’yan bindigar sun yi ta harbi don tsoratar da ’yan uwa da maƙwabta kafin su yi awon gaba da wanda suka yi garkuwan daga gidansu da ke Tse Aboh, Uchi-Mbakor a ƙaramar hukumar Tarka.
Ya kuma bayyana cewa, Kumashe ya koma gidansa ne bayan rasuwar ɗan uwansa wanda za a yi jana’izarsa a yau lokacin da masu garkuwar suka farwa gidan.
A halin da ake ciki, jami’ar hulɗa da jama’a ta Hukumar FRSC a Benuwe, Ngozi Ahula, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ƙara da cewa an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.