Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi
Published: 17th, February 2025 GMT
Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan.
Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa.
Ya shaida musu cewa a Facebook ya haɗu da ita, inda daga bisani ta ziyarci ɗakinsa a unguwar Olunlade a garin Ilori, bayan ta je wani biki.
Sai dai ya musanta zargin da ake masa na kashe ɗalibar mai suna Hafsah Yetunde Bello domin yin tsafi.
Jirgin soji ya kashe fararen hula a Katsina Malaman addini sun yi wa ’yan siyasa juyin mulki —Sule Lamiɗo Ku tona asirin ’yan tsubbu —Sarkin Ilori ga malaman addiniA cikin bidiyon tambayoyin da ’yan sanda ke wa matashin mai suna Abdulraham Bello, ya ce bayan zuwan budurwar tasa ne ya je ya sayo mata abinci, bayan ta bayyana masa cewa tana jin yunwa.
Ya shaida wa masu binciken nasa cewa bayan ya dawo daga sayo abincin ne ya iske ta tana shassheka a ɗakin.
“Ba a jima ba sai ta mutu. Ni kuma na tsotsa, babu wanda zan iya zuwa gaya wa ya taimaka min, shi ne ne sassara gawarta na yi mata gunduwa-gunduwa na je na jefar a wata bola a unguwar.
“A rikice nake, ban san abin da zan yi ba, ko tunanin wata hanya ta daban. Amma ban taɓa yin haka ba, wannan ne karon farko,” in ji matashin a ofishin ’yan sanda.
A cikin bidiyon da ya yi jawabin nasa cikin harshen Yarbanci ya bayyana cewa a halin yanzu yana neman gurbin karatu ne a Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Malete.
Mamaciyar dai ɗalibar aikin ƙarshe ce a Kwalejin Koyarwa ta Jihar Kwara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gunduwa gunduwa gunduwa gunduwa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.
Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.
Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.
“Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon bayan ku don tabbatar da cewa an sanar da jami’an gwamnati tare da karfafa gwiwar su bi wannan sabon tsari,” in ji shi.
Da yake mayar da jawabi, shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya yi alkawarin wayar da kan jami’an gwamnati cikin tsanaki game da muhimmancin bayyana kadarorin su, kamar yadda hukumar da’ar ma’aikata ta ba su umarni.
Ya tunatar da cewa rashin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa ne.
Dagaceri ya bada tabbacin bada goyon baya da hadin kai domin cimma burin da ake so na wannan shiri.
USMAN MZ