Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya  kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai.

A wata hira da tashar talabijin ta  “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya ce, ya na son Amurka ta mallaki ma’anadai na kasar  Ukiraniya a matsayin ladar da tallafin sojen da take bukata daga Amurka.

Gwamnatin Donald Trump ta gabatar wa da Kiev shawarar yin musayar ma’adanai na musamman da irinsu sun yi karanci a duniya, da take da su, na kaso 50%  da hakan zai zama abinda take biyan Amurka da su, madadin taimakon soje da take samu daga wajenta.

Sakataren Biatul-Malin Amurka Scott Bessent ne, ya gabatarwa da shugaban kasar Ukiraniya Volodymir Zeleski shawarar hakan a wata ganawa da su ka yi a ranar Larabar da ta gabata a birkin Kiev.

A karkashin wannan shawarar Amurkan za ta aike da sojojinta domin bada kariya ga wuraren hako wadannan ma’adanan a gabashin turai.

Tashar talabijin ta  NBC da ta watsa wannan labarin ta kuma ambato cewa, shugaban kasar ta Ukiraniya ya ki rattaba hannu akan yarjejeniyar ya kara da cewa, zai tuntubi jami’an gwamnatin kasar sa kafin haka.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.

A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar
  • Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha
  • Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata