NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba
Published: 4th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna.
Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu.
Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba.
NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son HaihuwaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi duba ne kan dalilan da suka hana samari yin ‘Ramadan Basket’ wannan shekarar.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ramadan ramadan basket Ramadan Basket
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi.
Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna.
Kwamandan NDA wanda tsohon dalibi ne a kwalejin ya bayyana jin dadinsa da yadda dalibai ke gudanar da ayyukansu ya yabawa mahukunta da ma’aikatan FGC Kaduna bisa yadda suke kiyaye ka’idoji.
A nasa jawabin shugaban kungiyar tsofaffin dalibai ta FGC Kaduna, Kwamared Seyi Gambo ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da gudummawar ta wajen daukaka darajar kwalejin ta hanyar daukar matakai na koyar da dalibai.
Shima da yake jawabi, shugaban taron kuma tsohon gwamnan jihar jigawa, Sanata Saminu Turaki ya bukaci dalibai da su tabbatar sun yi fice a fannin ilimi domin su zama masu amfani a cikin al’umma.
Shima da yake jawabi shugaban kwalejin gwamnatin tarayya ta Kaduna, Prince Adewale O. Adeyanju ya yi kira ga iyaye da su bada hadin kai ga hukumar makaranta domin ganin an kula da harkokin koyo.
An bayar da kyautuka na kyaututtuka da kudi ga daliban da suka kammala karatunsu da nagartattun dalibai da suka hada da malamai da suka kware sosai da kuma ma’aikatan da ba na koyarwa a kwalejin.
COV/SHETTIMA A.