Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa
Published: 23rd, March 2025 GMT
Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta.
Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta hanyar riƙe kyawawan halayenta na gaskiya da nagarta.
Gwamnan Gombe, ya kuma miƙa ta’aziyyar gwamnatinsa da mutanen jiharsa, ta hanyar addu’ar Allah Ya gafarta mata, Ya kuma sa Aljanna Firdausi ta zama makomarta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dikko Umar Radda Gwamna Inuwa Yahaya Gwamnonin Arewa Mahaifiya rasuwa ta aziyya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta ƙirƙiri ƙarin ƙananan hukumomi 29 a jihar.
Wata takarda da Aminiya ta samu ta nuna cewa Mukaddashin Mataimakin Magatakarda na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Musa Yerima, ya tura wannan ƙuduri zuwa Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, yana neman amincewar Majalisar Tarayya domin tabbatar da dokar a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ake yi.
Tinubu ya ƙirƙiri sabon harajin da zai iya ƙara N100 a kan kowacce litar man fetur Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — GwamnatiA halin yanzu, Jihar Bauchi na da ƙananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya amince da su.
Da ƙarin waɗannan 29 da ake nema, jihar da ke da kimanin mutane miliyan 10 za ta samu jimillar ƙananan hukumomi 49 ke nan.
A cikin wasikar da Mataimakin Magatakarda ya aike wa Sanata Barau Jibrin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Duba Kundin Tsarin Mulki, ya ce: “Ina farin cikin sanar da ku cewa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta amince da dokar da za ta ba da damar ƙirƙirar ƙananan hukumomi 29 a Bauchi, 2025.”
“Waɗannan ƙananan hukumomi ba za su fara aiki ba sai Majalisar Tarayya ta amince da dokar da za ta tabbatar da sunayen su kamar yadda Sashe na 8(5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya tanada.
“Na kwatanta wannan bugun da dokar da Majalisa ta amince da ita, kuma na tabbatar da cewa wannan kwafi daidai ne da dokar da aka amince da ita,” in j wasikar.
Sunayen sabbin ƙananan hukumomin da ake son kirkira sun haɗa da: Balma, Bauchi ta Gabas, Bauchi ta Yamma, Beshongo, Bula, Burra, Chinade, Dagauda/Jalam da Disina.
Sauran su ne: Dogon Jeji/Jurara, Dass ta Yamma, Gadau, Galambi, Ganjuwa ta Gabas, Girawa, Gololo, Gwana, Isawa, Jama’a, Kankara, Lame, Lere, Madara, Sade, Sakuwa, Saye, Udubo, Yankari da Zungur.
Hedikwatocinsu sun haɗa da: Nasaru, Cibiyar Mata, Miri, Beni, Bununu, Chinade, Dagauda, Disina, Dogon Jeji, Lukshi, Gadau, Kangere, Faggo, Gololo, Futuk, Isawa, Nabordo, Akuyam, Karkara, Lame, Lere, Madara, Sade, Sakuwa, Hardawa, Udubo, Yelwan Duguri da Liman Katagum.
Yerima ya ƙara da cewa: “Wannan dokar an tura ta zuwa Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Duba Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Tarayya domin ci gaba da matakan da suka dace.”