Aminiya:
2025-03-15@23:55:40 GMT

Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’

Published: 9th, March 2025 GMT

Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci.

Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar.

Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai

Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin al’ummar Musulmi.

A jawabinsa bayan buɗa-bakin azumi, Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kyautata jin daɗin malaman Tsangaya da kuma yara Almajirai.

Ya bayyana muhimmancin ilimin Alƙur’ani ga al’umma tare da jaddada buƙatar samar da yanayi mai ɗaukaka koyo da koyarwa.

Gwamnan ya yi bayanin yadda gwamnatinsa ta yi gagarumin ƙoƙari wajen gina manyan makarantun Tsangaya da ƙananan makarantun Almajirai a faɗin jihar, tare da haɗa ilimin Alƙur’ani da na zamani cikin tsarin karatu.

Haka kuma, ya yi nuni da cewa yara Almajirai an sanya su cikin shirin lafiya na Go-Health, wanda ke ba su damar samun kulawar lafiya kyauta domin tabbatar da lafiyarsu.

“Mu a matsayin gwamnati mun fahimci muhimmiyar rawa da makarantun Tsangaya ke takawa wajen tarbiyya da cigaban ilimi ga yaranmu.

“Wannan ne ya sanya muka fifita jin daɗinsu ta hanyoyi daban-daban, ciki har da gina makarantun Tsangaya da kuma shigar da su cikin shirin Go-Health domin samun ingantacciyar kulawar lafiya ba tare da wata matsala ba,” in ji Gwamna Inuwa.

Da yake magana a madadin malaman Tsangaya, Goni Mai Babban Allo ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya kan goyon bayan da yake bayarwa ba dare ba rana.

Ya kuma bayyana cewa Gwamnan ya ɗauki matakai na musamman, ciki har da gina makarantun Tsangaya, sanya fitilu masu aiki da hasken rana a makarantun, da haɗa Almajirai cikin shirin kula da lafiya na jihar Gombe.

“Ba mu taɓa samun gwamnati da ta damu da jin daɗin malaman Tsangaya da ɗalibanmu kamar wannan ba,” in ji Goni Mai Babban Allo.

A cikin girmamawa ga ƙoƙarinsa da kuma sadaukarwarsa, Ƙungiyar Alarammomi ta naɗa Gwamna Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’, alamar kasancewarsa bawan Alƙur’ani mai sadaukarwa.

Tun da farko, a jawabinta na maraba, Sayyada Amina Sheikh Dahiru Bauchi, mai bai wa gwamna shawara ta musamman kan harkokin Tsangaya da Ilimin Almajiranci, ta yi kira ga Alarammomi da su ƙara yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Inuwa Yahaya jihar Gombe malaman tsangaya Gwamna Inuwa Yahaya makarantun Tsangaya malaman Tsangaya a makarantun Tsangaya da

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas Ta Yi Gargadin Bullar Yunwa A Gaza A Cikin Watan Ramadan

Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi akan cewa; Wata sabuwar yunwa za ta  bulla a Gaza saboda yadda HKI take ci gaba da killace yankin da hana shigar da kayan agaji hatta a cikin watan Ramadan.

Kakakin kungiyar ta Hamas Abdullatif al-Qa’uni wanda ya fitar da wani bayani ya ce; Falasdinawa a yankin Gaza an killace su, makonni biyu a jere, kuma sojojin mamaya sun hana a shigar da kayan abinci,magunguna, da makamashi, wanda hakan yake a matsayin amfani da yunwa a matsayin makamin.

Qa’ani ya kara da cewa; Abinda ‘yan mamaya suke yi, shi ne jefa Falasdinawa cikin yunwa. Haka nan kuma ya ce;  A nan gaba kadan kayakin da ake da su na bukatun yau da kullum za su kare a cikin Gaza, wanda hakan zai kara wahalar da mutanen yankin.

Kakakin kungiyar ta Hamas ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi matsin lamba akan HKI domin bude iyakoki da bayar da damar shigar da kayan agaji.

Tun a farkon wannann watan Maris da muke ciki ne HKI ‘yan mamayar su ka hana shigar da muhimman kayakin da ake bukata zuwa cikin yankin na Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi
  • Matsalar Tsaro: Shugaban Ƙaramar Hukuma ya tabbatar da haɗa kai da Sarakuna
  • Inganta Tsaro: Gwamna Nasir Ya Bai Wa Jami’an Tsaro Motocin Sintiri A Kebbi
  • Hamas Ta Yi Gargadin Bullar Yunwa A Gaza A Cikin Watan Ramadan
  • 2027: Na Shirya Tsaf Don Yin Aiki Tare Da Peter Obi Don Ceto Ƙasar Nan, Gwamnan Bauchi
  • Peter Obi Ya Ziyarci Bauchi, Ya Gana da Gwamna Bala Mohammed
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Rukuni Na Farko Na Masu Tsaron Makarantu
  • Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi
  • Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Nada Kwamishina
  • Yadda ’yan Boko Haram suka sha da ƙyar a hannun tawagar Gwamna Zulum