Shugaban Masar Ya Dage Ziyararsa Zuwa Amurka Har Sai Bayan Zaman Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa
Published: 14th, February 2025 GMT
Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa
Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu.
Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka na neman korar Falasdinawa da suke zaune a Zirin Gaza zuwa hijira da nufin kwace musu kasarsu ta hanyar dabarar siyasa.
A wani labarin kuma, majiyoyin Masar da suke Amurka sun bayyana cewa: Ma’aikatar tsaron Amurka ta “Pentagon” ta shiga cikin jerin masu barazanar ga Masar matukar ta ki amincewa da shawarar Trump na neman korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, wanda ke nufin kwace wa Falasdinawa kasarsu, kamar yadda shafin yanar gizon Al-Araby Al-Jadeed ya bayyana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Matsin Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Sun Rage Zuwa Kasashen Waje
Lamarin ya ci gaba da raguwa har zuwa 2024, inda yawan kudaden da ake kashewa a yawon ketare ya fadi da kaso 14 a matakin shekara-shekara zuwa dala biliyan 2.66.
Hakan na nuni da cewa ‘yan Nijeriya sun rage kashe kudaden da suke kashewa kan safarar jiragen sama da dala biliyan 1.12 ko kuma kashi 30 cikin dari a cikin shekaru biyun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp