DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah
Published: 26th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A duk lokacin da aka ce bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan al’amura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shi ne na farashin kayayyakin masarufi.
A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin masarufi gabanin bikin sallah.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: farashin kayan masarufi
এছাড়াও পড়ুন:
Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
Daga Salihu Tsibiri
Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.
Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki.
Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas.
Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa su ma gwamnoni suna da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gwamnatin tarayya, lokaci ya yi da za a duba batun tsaro a matsayin barazana da ba ta da alaƙa da jam’iyya, addini ko ƙabila.
Ya kara da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da ta’azzara, akwai bukatar a rufe majalisa gaba ɗaya tare da ayyana dokar ta-baci, har sai an ɗauki matakin gaggawa don kare ƙasar daga halin da take ciki.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ’yan sanda, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, inda ya yaba wa umarnin shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga wasu manyan mutane domin ƙara ƙarfi a yaki da laifuka a fadin ƙasar.
Sai dai Makki Yalleman ya yi kira da a samar da isasshen kuɗi da na’urorin zamani domin inganta ƙwarin gwiwa da ƙwarewar rundunar ’yan sandan Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ’yan bindiga.
A nasa bangaren, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya danganta matsalolin tsaro da ake fuskanta ga gazawar bangarorin gwamnati uku wajen tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, musamman kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da kuma masu yi wa gwamnati tawaye.