HausaTv:
2025-08-01@09:47:04 GMT

IRGC: Za Mu Kai Farmakin “ Wa’adus-Sadik” Na 3 Akan ‘Yan Mamaya

Published: 18th, February 2025 GMT

Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran “IRGC” ya sanar da cewa; Iran za ta kai farmakin “Wa’adus-Sadik 3”  a lokacin da ya dace.

Laftanar janar Ali Fadwi ya kuma yi ishara da yakin Gaza, yana bayyana cewa, su kansu ‘yan sahayoniya sun bayyana cewa Hamas ta yi nasara, su kuma ba su cimma manufarsu ba.

Iran dai ta kai wa HKI hare-hare guda biyu a aka bai wa Sunan                    “ Wa’adussadik” na daya da na biyu. Hare-haren na Iran dai sun kasance mayar da martani ne akan harin da HKI ta kai wa  karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Syria da kuma kashe mata jami’an soja masu bayar da shawara ga gwamnatin Damascuss. Na biyun kuwa ya kasance mayar da martani akan kisan gillar da ‘yan sahayoniyar su ka kawo a Tehran wanda ya yi sanadiyyar shahadar shugaban kungiyar Hamas Shahid Isma’ila Haniyyah.

A wani gefen, shugaban kungiyar Hamas a yankin Gaza, Khalil Hayyah ya fada a makon da ya shude cewa; Iran ta kasance a sahun gaba wajen taimakawa gwgawarmayar Falasdinu, kuma muna da tabbacin cewa za ta cigaba da yin hakan.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu

Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba.

 

Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke.

 

A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin Farfesa Yusuf Gana Balami a matsayin Shugaban Hukumar Ilimin Sakandare ta Jihar Borno.

 

Balami, Farfesa a fannin ilimi, ya fito ne daga Hawul da ke kudancin jihar.

 

Zulum ya taya Balami murna tare da bukatar sa da ya yi amfani da shekarunsa na gogewa a fannin ilimi, a matsayin shugaba a bangaren gudanarwa da karantarwa wajen sake fasalin ilimin sakandare a jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar
  • Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu
  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba
  • Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  •  Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta
  • Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba