Qatar Ta Ce Bata Goyon Bayan Yakin Don Warware Shirin Nukliyar Kasar Iran
Published: 8th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani, ya kara nanata matsayin kasar na kin duk wani yaki kan shirin Nukliyar kasar Iran, ya kuma yi kira ga Amurka da Iran su warware wannan matsalar ta ruwan sanyi. Ko hanyar diblomasiyya.
Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa shirinta na makamashin na zaman lafiya ne.
Mohammed bin Abdulrahman Al Thani yace “akwai bukatar kasashen Iran da Amurka su fahinci juna a cikin wannan batun” sannan ya sake nanata cewa Qatar bata goyon bayan yaki. Sannan daga karshe yace matsalar nukliyar kasar Iran ta zama abinda damuwa ga dukkan kasashen yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar IAEA ta yi ishara da yiwuwar sake komawa teburin tattaunawa tare da Iran
Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in kasar Iran a baya-bayan nan, ba a samu wani ci gaba kadan ba a cikin binciken nukiliyar da aka shafe shekaru ana yi kan kasar Iran, yana mai jaddada bukatar gaggauta warware takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin Tehran da Washington.
A wata hira da Bloomberg babban darektan hukumar Rafael Grossi ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai koma Tehran domin ci gaba da tattaunawa da jami’an Iran. “Muna kan wani muhimmin mataki,” in ji Grossi, yana mai cewa wadannan tattaunawa za su iya taka muhimmiyar rawa a nan gaba.
Grossi ya kara da cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya aike da wasika zuwa ga jagoran ruhin Iran, wanda ke nuni da bukatar cimma fahimtar juna da ke musanta yuwuwar Iran ta mallaki makamin nukiliya.
A sa’i daya kuma, Grossi ya jaddada bukatar shugabannin kasashen duniya su yi taka-tsan-tsan da kamewa, a daidai lokacin da ake ci gaba da tafka mahawara ta kasa da kasa game da bukatar dakile makaman nukiliya.
A cikin jawabinsa, Grossi ya bayyana cewa, duniya na fuskantar kalubale guda biyu: a bangare guda, akwai batutuwan da ba a warware su daga baya ba, a daya bangaren kuma, damar da ta kunno kai na cimma wata yarjejeniya nan gaba da za ta kai ga cimma matsaya kan batun nukiliyar Iran na dogon lokaci.