Gwamna Umar Namadi Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Sallah Karama
Published: 31st, March 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.
Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar.
Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan na Ramadan.
Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabanni jagorancin don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma.
Namadi ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Radiyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan ya kuma karɓi manyan baki da suka kai masa gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu.
Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara.
A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata.
A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama.
Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.