Lin Jian Ya Yi Bayani Kan Takardar Bayani Game Da Shawo Kan Sinadarai Masu Alaka Da Sinadarin Fentanyl Ta Sin
Published: 5th, March 2025 GMT
A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar da fasahohin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa.
Dangane da wannan takardar da kasar Sin ta fidda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, takardar za ta ba da taimako ga al’ummomi da gamayyar kasa da kasa wajen kara musu fahimtar matsayin kasar Sin kan wannan batu, da matakan da Sin ta dauka, da kuma nasarorin da Sin ta cimma a wannan fanni. Kasar Amurka ta yada jita-jita kan batun Fentanyl domin bata sunan kasar Sin, tare da kara haraji kan hajojin kasar Sin bisa wannan hujja. Babu sanin ya kamata cikin wannan lamarin. Amurka ta cutar da wasu da kai karan kanta.
Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin Jiangsu Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin JiangsuA sa’i daya kuma, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da Amurka bisa ka’idar nuna adalci da girmama juna, kuma tana adawa da dukkan irin matakan da Amurka ta dauka domin matsa wa kasar Sin lamba, bisa hujjar batun Fentanyl. Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta gaskiya, da kare moriyar kanta yadda ya kamata, domin gudanar da harkoki ta hanyoyi masu dacewa.
Lin Jian ya kara da cewa, Amurka ta sake kara haraji kan hajojin Sin bisa hujjar batun Fentanyl, kana, sau da dama, kasar Sin ta nuna adawa kan wannan batu. Dukkanin matakan mayar da martani da kasar Sin ta dauka sun kasance matakan da suka wajaba kuma masu dacewa domin kare moriyar kasa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Sin ta
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu.
A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man fetur da sinadarai don samar da kudaden gudanar da ayyukanta na tabarbarewar zaman lafiya, da kungiyoyin da ya bayyana da na ta’addanci to Amurka za ta dauki matakin laftawa Iran da dukkan kawayenta alhakin kaucewa takunkumi.”
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Iran ta sanar da cewa za a sake gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da gwamnatin shugaba Donald Trump a birnin Rome a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a karkashin jagorancin kasra Oman.