Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
Published: 23rd, February 2025 GMT
Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu.
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labaru na yau da kullum.
A wajen taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla tsakanin Amurka da kungiyar EU. A yayin da yake ba da amsa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana ba da shawarar cewa, ya kamata dukkan bangarori su warware bambance-bambancen tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tattaunawa, domin kiyaye yanayin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa.
Bugu da kari, dangane da taron tattauna batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a kasar Sweden, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya a bayyane yake. Ana sa ran Amurka za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen aiwatar da muhimman shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Game da rikicin kan iyakar kasashen Cambodia da Thailand, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya da adalci, da ci gaba da yin cudanya da kasashen Cambodia da Thailand, da sa kaimi ga zaman lafiya da tattaunawa.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp