Bankin Duniya : Sake Gina Lebanon Yana Bukatar Dala Biliyan 11
Published: 8th, March 2025 GMT
Bakin duniya ya kiyasta cewa ana bukatar dala biliyan 11, domin sake gina Lebanon sakamakon barnar da hare haren Isra’ila suka haifarwa kasar.
Bangaren gidaje na Lebanon ya fi fama da matsalar, inda aka kiyasta asarar da ta kai dala biliyan 4.6, yayin da masana’antar yawon bude ido ta yi asarar dala biliyan 3.
“Sakamakon rikice-rikicen ya haifar da raguwa a ainihin GDP na Lebanon na 7.1 bisa dari a 2024,” in ji Bankin Duniya.
Rahoton ya kara da cewa, “Ya zuwa karshen shekarar 2024, raguwar GDP na kasar Lebanon tun daga shekarar 2019 ya kusan kashi 40%, wanda hakan ya haifar da koma bayan tattalin arziki a bangarori da dama da kuma yin tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar.”
Sojojin Isra’ila sun fara kai farmaki kan sansanonin Hizbullah a kudancin Lebanon jim kadan bayan kaddamar da kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yiwa kawanya a watan Oktoban shekarar 2023.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu.
Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara.
A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata.
A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama.
Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.