Guterres Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimaka Wa Sudan
Published: 16th, February 2025 GMT
Babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji.
Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake bukatuwa da su, domin taimakawa mutanen kasar ta Sudan da yaki ya daidaita.
Babban magatakardar MDD ya yi ishara da rawa ta jarunta da kungiyoyin mata suke yi a cikin yanayi mai hatsari,tare dayin kira da a kare rayukan fararen hula.
Har’ila yau ya yi kira da a kawo karshen shigar da makamai zuwa kasar ta Sudan da bai wa zaman lafiya dama, a cikin watan Azumin Ramadana mai shigowa.
A mako mai zuwa ne dai MDD za ta kaddamar da gidauniyar agaji ta neman kudaden da za su kai dala biliyan 6 domin taimakawa miliyoyin mutanen Sudan da suke zaman hijira a kasashe makwabta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA