HKI Tana Cigaba Da Hana Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Yankin Gaza
Published: 17th, February 2025 GMT
Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta.
Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan.
Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin Jordan fiye da wadanda Falasdinawa suke ginawa.
Wannan matakin na HKI yana zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Robio yake ziyara a Tel Aviv, kuma a lokacin da Amurkan ta bai wa HKI bama-baman MK-84 har guda 1,800.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
Hukumar ba da agaji da kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta “UNRWA” tana karkashin wuta sakamakon ma’aikatan 330 da suka yi shahada kuma aka lalata cibiyoyinta 300 a Gaza!
Inas Hamdan, mai magana da yawun hukumar ta UNRWA a birnin Alkahira, ta tabbatar da cewa; Yunwar da ke faruwa a zirin Gaza, wani bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya shafi mutane sama da miliyan biyu, ciki har da akalla yara miliyan daya. Wannan ya saba wa duk dokokin jin kai da ka’idoji, kuma abin takaici, lamarin yana da kara muni.
Hamdan ta yi nuni da cewa, a lokacin da suke magana kan matsalar agajin jin kai ko shigar da kayan abinci zuwa zirin Gaza, suna fuskantar shamaki da aka sanya a zirin Gaza, baya ga tsarin rabon da wata gidauniya mai suna Gazan Humanitarian Foundation ke gudanarwa, wanda ke zama tarkon mutuwa. Ya zuwa yanzu, fiye da mutane dubu sun mutu yayin da suke jiran abinci, haƙƙin duk mazauna cikin wannan mawuyacin yanayi.
Ta yi gargadin cewa matakan karancin abinci na ci gaba da tabarbarewa, inda ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba da kuma matukar damuwa. Adadin matsalolin rashin abinci mai gina jiki, musamman a tsakanin yara, yana nuna mummunar tabarbarewa a wannan fanni. Akalla yara 5,500 ‘yan kasa da shekaru biyar ne ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, ciki har da yara akalla 800 da ke cikin matsanancin hali na rashin abinci mai gina jiki, ma’ana suna fuskantar barazanar yunwa.