Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya
Published: 23rd, February 2025 GMT
Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan kwangilar da hukumar ta rattaba wa hannu kan hidima ga Alhazan Nijeriya a Masha’ir a lokacin aikin Hajjin 2025.
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.