Isra’ila : ‘Yan adawa sun kira zanga-zangar gama-gari bayan korar shugaban Shin Bet
Published: 23rd, March 2025 GMT
Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.
Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.
“Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi.
A ranar Juma’a ne Kotun kolin Isra’ila ta dakatar da matakin da gwamnati ta dauka na korar shugaban Shin Bet, Ronen Bar, wanda ba a taba ganin irinsa ba, wanda sanarwar korar tasa ta sake haifar da baraka a tsakanin al’umma.
Amma Netanyahu ya dage kan cewa,”Ronen Bar ba zai ci gaba da zama shugaban Shin Bet ba, ba za a yi yakin basasa ba, kuma Isra’ila za ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa ta dimokuradiyya,” in ji shi a cikin wani sakon bidiyo inda yake kalubalantar Kotun Koli.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu.
Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai.
Sun bayyana shi a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya yi namijin kokari wajen inganta tattaunawa tsakanin addinai da hadin kan kasa.
Kungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa, da fadar shugaban kasa, da sauran al’ummar Nijeriya da su goyi bayan nadin, inda ta ce hakan zai karfafa cibiyoyin gargajiya da kuma samar da hadin kai a tsakanin sarakunan gargajiya a fadin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp