Yadda ’yan bindiga suka sace ɗalibai 4 a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma
Published: 3rd, March 2025 GMT
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina.
’Yan bindigar sun sace daliban ne a ɗakunan kwanansu da ke yankin Paris Quarters a garin na Dutsinma.
Maharan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kutsa yankin ne da misalin ƙarfe 4 an asubahin ranar Lahadi, suka yi awon gaba da ɗaliban.
Jami’an tsaro sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa, amma kafin su isa wurin ’yan bindigar sun riga sun riga sun tsere da ɗaliban.
Dutsinma na daga cikin ƙananan hukumomin Jihar Kastina da suka fi dama da matsalar ’yan bindiga da ke satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, duk kuwa da matakan da gwamnati da kuma hukumomin tsaro ke ɗauka.
Duk da cewa zuwa lokacin da muka samu wannan labari kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq, ko gwamantin jihar ba su fitar da sanarwa ba, amma wasu majiyoyin tsaro sun ce jami’an tsaro sun fara farautar maharan da nufin kuɓutar da ɗaliban cikin aminci.
Ana yawan samun matsalar garkuwa da ɗalibai musamman ba manyan makarantu a sakamakon matsalar rashin tsaro.
A watan Afrilun 2021 an sace ɗalibai kimanin 20 da ma’aikata biyu a Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna.
Daga bayan aka tsinci gawar uku daga cikin ɗaliban kafin daga bisani bayan watanni aka sako ragowar 14 da ke hannun ’yan bindiga.
Kazalika an sace ɗalibai da dama a Jami’ar Tarayya ta Gusau, waɗanda sai bayan tsawon lokaci aka sako su.
A watan Mayun 2024 aka sace ɗalibai tara daga Jami’ar Tarayya ta Confluence da ke Jihar Kogi a cikin aji.
Ƙo a watan Fabrairun 2025 a sace da ɗaliban Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi, Jihar Binuwai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jami ar Tarayya a Jami ar Tarayya sace ɗalibai da ɗaliban yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu 32 A Katsina
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp