2025-09-18@18:35:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5302
«lambar yabo»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya jagoranci jerin gwanon zuwa gidan Sarkin Ladanai na Zazzau a matsayin al’adar tarihi na bikin Mauludin na bana. Bikin Mauludin na bana shi ne karo na 185 da aka shirya a hukumance da aka gudanar a Zariya. An kama mace ɗauke da bindiga da N2m a otal Mauludi: ’Yan sanda sun haramta hawa babur da daddare a Gombe Sarkin da ya hau kan doki ya samu rakiyar ’yan uwa na masarautar domin yin mubaya’a ga fitaccen gidan malamin addinin Musulunci, wato gidan Sarkin Ladanai. An gudanar da bukukuwan murnar ne don zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Manyan Malaman Addinin Musulunci sun gudanar da addu’o’i a harabar domin samar...
Bayan sama da shekaru biyu a kan mulki, gwamnatin Sakkwato ta fara waiwayar ’yan gudun hijira da hare-haren ’yan bindiga suka raba da muhallansu. A dukkanin ƙananan hukumomi 23 na jihar akwai ’yan gudun hijira da ke buƙatar ɗauki. Tsohon mataimakin Gwamnan Gombe da wasu jiga-jigai sun fice daga PDP zuwa APC Saudiyya ta ƙaƙaba wa masu laifukan rashin ɗa’a sabuwar tara Wasu ma sun tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar, inda suka yada zango a jihohin Dosso, Maradi da Tahoua. Mutane da dama, musamman yara, suna cikin mawuyacin hali. Wasu marayu suna yin sana’o’i kamar tuƙa baro, tara dutse ko yin bara domin samun abin ci, ba tare da wata kulawa daga gwamnati ba. Da yawa daga cikinsu ba sa zuwa...
Wanda aka kama sunansa iro Garba mai shekaru 25 daga Zangwaye Fulani a ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano. Ya amsa cewa shi da wasu mutane huɗu sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi. An kuma samu rigunan sojoji guda uku a hannunsa. Kwamishinan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran mutane huɗun da ake zargi da hannu a garkuwar da ta faru a Sumaila, da ke Jihar Kano. A wani lamari kuma, ’yansanda sun kama mutane huɗu da ake zargi da fasa shago a ƙaramar hukumar Malam Madori. Waɗanda aka kama sun haɗa da: Nuhu Yusif Saleh (19), Hassan Ibrahim (19), da Nura Musa (22). An ƙwato akwati mai ɗauke da kuɗi Naira 870,000,...
tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce hare-haren da aka kai kan masu gudanar da taro a jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi a matsayin abubuwan da ke da haɗarin “jefa Najeriya cikin tsarin kama-karya a karkashin gwamnatin Bola Tinubu.” A karshen makon da ya gabata ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kai hari tare da tayar da tarzoma a wani wurin taron yayan jam’iyyar hadaka ta ADC a birnin Kaduna. Cikin mahalarta taron har da jiga-jigan jam’iyyar ta ADC, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kuma shugaban jam’iyyar na Arewa maso yamma. Daga baya, a jiya Alhamis rundunar yansandan Najeriya a jihar ta Kaduna ta aika da takardar gayyata ga jam’iyyar ta...
Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya. Kwanan nan, Maroko ta karbi bakuncin taron bita na farko, kan kula da lafiyar yara, yayin da Lebenon kuma ta kafa kwamitin kula da cutar kansar yara, wanda ya shafi wadanda suka tsira da rayukansu, ma’aikatan jinya, sauran ma’aikata da kuma wakilan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a yau Juma’a, shugaba Amurka Donal Trump zai rattaba hannu kan wata doka da za ta sauya sunan ma’aikatar tsaron kasar zuwa ma’aikatar yaki. Canjin suna na dindindin na buƙatar Izinin majalisa, to amma umarnin zartarwa da shugaban zai sa wa hannu, zai ba da damar amfani da sunan na wucin gadi. A wata hira da aka yi da shi, sakataren tsaron kasar Pete Hegseth, ya ce hakan zai nuna wani sauyi da ke nufin ma’aikatar tsaron kasar ta Pentagon ta rungumi wani suna na Jarumta. Ya ce ko nasarorin da kasar ta samu a yakin duniya na daya da na biyu ta same su ne da sunan Ma’aikatar Yaki, ba wai...
A ranar 3 ga watan Satumba, Sin ta gudanar da babban bikin faretin soja a birnin Beijing, don tunawa da cika shekaru 80 da yakin da Sinawa suka yi da mamayar Japan kana yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Wannan bikin faretin soja ya nuna sabbin makamai na zamani na Sin, wadanda suka nuna ci gaban fasahohin tsaron kasar. Bikin da kuma kayayyakin aikin soja na zamani sun sa wasu mutane shakku: Shin Sin za ta kama hanyar nuna fin karfi? Amsar ita ce, a’a. Kamar yadda wani soja da ya halarci bikin ya ce: “Ba karfi muke nuna ba, sai dai niyyarmu ta kare adalci.” A wannan bikin faretin soja, rukunin sojojin kiyaye zaman lafiya, ya ja hankalin al’umma...
Rahotanni sun bayyana cewa sanar da sabon kwamandan hedkwatar khatamul ambiya na nuna irin sabbin canje –canje da irin tsari da ta bullo da shi kan abubuwan da ta fi bawa muhimancin, kuma wata babbar cibiya da ake sa ido kan tsaron kasa, canjin jagoranci na iya yin tasiri babba a bangaren soji wajen tunkarar kalubalen da take fuskanta a bangarori daban daban. Major ganaral Ali Abdullahi sabon kwamandan hekdawatar khatamul Ambiya ya jaddada a bayanin da ya fitar cewa sojojin kasar Iran a shirye suke su kare kasar daga duk wata barazana, da kuma kare dukkan ababen girmamawa na kasar, Ya kara da cewa a halin yanzu sojojin kasar sun fi zama cikin shirin ko ta kwana fiye da...
Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin yaki da zalunci da danniya da Jama’ar Sinawa suka yi, ya sa kasar ta kudiri aniyar yaki da zalunci da danniya a duniya ta rungumi manufar tabbatar da zaman lafiya, inda ta nuna wa duniya cewa, lokacin wariya da danniya, tsarin rayuwar dabbobi (na sama ya buge na kasa), ba zai dore ba amma samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro, na sama ya yi...
Karamar karamar hukumar Jibiya ita ce ta fara shirya taro domin yin sulhu da ‘yan bindigar, sai dai kuma ba a ga wakilin gwamnatin Jihar Katsina a wannan sulhu ba, amma dai an ga shugaban karamar hukumar da sauran jami’an tsaro da ake zargin daga Abuja suke halartar irin wannan taro. An yi wannan sulhu a karamar hukumar Jibiya kimanin wata hudu da suka gabata, kuma al’amurra na ci gaba da tafiya yadda ake so, zuwa yanzu dai al’ummomi a wannan karamar hukumar na ci gaba da harkokinsu kamar ba a yi tashin hankalin ‘yan bindiga ba. Kar a manta duk lokacin da aka yi irin wannan taro gwamnatin Jihar Katsina na cewa babu hannunta kuma ba da ita aka...
An samu sauyi a siyasar Jihar Gombe, yayin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mista Tha’anda Jason Rubainu, tare da babban jigon jam’iyyar PDP, Mista Jerry Damara, suka sauya sheƙa zuwa APC. Rubainu, wanda ya yi mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo daga 2011 zuwa 2015, ya hada kai da Damara da kuma wasu manyan ’ya’yan jam’iyyar PDP daga yankin Kuancin Gombe. Mauludi: ’Yan sanda sun haramta hawa babur da daddare a Gombe Gwamnatin Yobe za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata’ala Yayin da yake miƙa katin shaidar shigarsa APC ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Mista Damara, wanda shi ne shugaban Mesotho Group Limited, ya ce dalilin sauya sheƙarsu shi ne kyawawan ayyukan raya ƙasa da gwamnan...
An samu sauyi a siyasar Jihar Gombe, yayin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mista Tha’anda Jason Rubainu, tare da babban jigon jam’iyyar PDP, Mista Jerry Damara, suka sauya sheƙa zuwa APC. Rubainu, wanda ya yi mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo daga 2011 zuwa 2015, ya hada kai da Damara da kuma wasu manyan ’ya’yan jam’iyyar PDP daga yankin Kuancin Gombe. Mauludi: ’Yan sanda sun haramta hawa babur da daddare a Gombe Gwamnatin Yobe za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata’ala Yayin da yake miƙa katin shaidar shigarsa APC ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Mista Damara, wanda shi ne shugaban Mesotho Group Limited, ya ce dalilin sauya sheƙarsu shi ne kyawawan ayyukan raya ƙasa da gwamnan...

‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido
“Tun lokacin Buhari har zuwa yanzu lokacin Tinubu, ‘yan Nijeriya na cikin wahala. Talauci tana nan a ko’ina, matasa ba su da aikin yi, kuma tattalin arziki yana lalacewa. Su na cewa suna yaki don Nijeriya, amma a zahirin gaskiya, suna yaki ne kawai don kansu da aljihunsu. “Na kasance cikin gwagwarmaya tun daga shekarun 1970. Na san ma’anar yakki don samun dimokuradiyya da kuma don talakawa. Gwamnatin Tinubu, kamar dai gwamnatin Buhari take ta gaza warware matsalolin ‘yan Nijeriya. Maimakon a samu sauki, sai aka samu karuwar cin hanci da rashawa da wahallalu da kuma amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba,” in ji Lamido. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, tsohon shugaban kungiyar masu tsara gidaje a Nijeriya, Aliyu Wammako, ya ce, rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu na shafan tattalin arziki sosai. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ka da ta tsaya bata wani lokaci ta kama biyan ‘yan kwangila kudadensu da hakan zGwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da wani kwamiti da zai tattauna batun basussukan da suka dabaibaye harkokin jakadancin Nijeriya a kasashen ketare. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje, Kimiebi I. Ebienfa, shi ne ya shaida hakan ya cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Abuja. Ebienfa ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden da aka tura domin...
Amir Saeed Iravani jakadan kasar Iran a MDD ya bukaci kasashen duniya su yi allawadai da hare-haren da aka kaiwa cibiyoyin makamashin nukliya ta kasar Iran, a kuma gurfanar wadanda suka yi hakan gaban kuliya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a yau Jumma’a a MDD, yace abinda ya faru a yakin kwanaki 12 ya tana hankalin kasashen duniya tare da sanya ayar tambaya kan yadda shirin makamashin Nukliya na zaman lafiya a duniya na wata kasa. Har’ila yau wannan ya sanya shakka a kan zaman lafiya a duniyar da take ciki da makaman nukl;iya. Har’ila yau da makomar yarjeniyoyi kan makaman kare dangi. Wadanda suka hada da NPT da sauransu. Hare-haren da...
Shugaban kungiyar Hamas Khalil Al-Hayya da kuma wasu manya-manyan shuwagabannin kungiyar Hamas a Gaza, sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas arachi a yau a birnin Doha na kasar Qatar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan haduwar itace ta farko tun bayan yakin kwanaki 12 kan kasar Iran wanda HKI tayi, wanda kuma yake nuna irin yadda gwamnatin JMI ta damu a al-amarin Falasdinawa. A baya-bayan dai kasashen duniya da dama sun bayyana anniyarsu ta bayyana goyon bayansu ga kafa kasar falasdinu mai cikekken yanci, mai kuam zaman kanta a babban taron shuwagabanni kasashen duniya a babban zauren majalisar dinkin duniya a cikin wannan watan da muke ciki. Daga cika har da wasu...
“Ma’aikatar ba ta yi shiru ba kan irin takunkumin da iyakace kudi ya sanya a tafiyar da ayyukan ofisoshin, ciki har da rashin iya biyan albashin ma’aikatan gida, biyan bukatun kudi ga masu bayar da ayyuka, haya ga masu gidaje, da kuma alawus ga jami’an da ke aiki a gida,” in ji sanarwar. Yayin da ta jaddada cewa wannan yanayi na nuna halin tattalin arzikin kasa gaba daya, ma’aikatar ta lura cewa karancin kudi a tsawon shekaru ya ragi ikon ofisoshin wajen gudanar da manyan ayyukan diflomasiyya. “Dole ne a bayyana, duk da haka, cewa ofisoshin diflomasiyyar Nijeriya ba su da kariya daga halin tattalin arzikin gida da kalubalen da ke tattare da ayyukan gwamnati. Matsalar kudi a...
Dr. Shuaibu ya ce maganganun El-Rufai na baya-bayan nan, ciki har da zargin da ya yi a talabijin na kasa cewa gwamnati ta tarayya da ta jihar na “ba wa ‘yan ta’adda cin hanci,” karya ne, mai hadari, kuma an yi su ne don raunana kokarin tsaro. Ya kara da cewa Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaron (ONSA) ya riga ya musanta wannan zargi a matsayin mara tushe. Ya ce hukumomin tsaro da shirye-shiryen cikin gida sun samu nasarori masu yawa a karkashin gwamna Uba Sani, inda ya bayar da misalin cafke manyan shugabannin ‘yan ta’adda da kuma dawo da kwanciyar hankali a yankunan da ke cikin tashin hankali kamar Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da Kachia....
A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak. BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.” Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da * Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano. Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi...
A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak. BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.” Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da * Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano. Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi...
Kamfanin sadarwa ta Google a halin yanzu tana aiwatar da yakin farfaganda ga Natanyahu a shafukan yanar gizo da kuma dukkan kafafen da kamfanin yake da shi don kyautata fuskar Natanyahu da kuma HKI a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, aikin wanda Natanyahu ya sayeshi da dalar Amurka miliyon 45 zai rage irin kiyayyar da ake masa a duniya da kuma gwamnatinsa. Sannan mai yuwa ya rage irin takurawa da ake masa kan kissan kiyashin da sojojinsa suke aikatawa a gaza da kuma kasar Falasdinu da suka mamaye. Daga karshe dai gwamnatin Natanyahu ya fake da farfaganda ta karya don wanke faska da hannayensa tare da amfani da kamfanin google don boye aiyukan ta’adanci...
Dan Majalisar Wakilai na mazabar Kiru/Bebeji daga jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce ba zai zama abin mamaki ba idan ya fice daga jam’iyyar. Ya kuma ce da arzikinsa ya shiga tsarin Kwankwasiyya, kuma ya bauta mata da kudinsa kamar yadda ita ma Kwankwasiyyar ta taimake shi. ’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi A tattaunawarsa da DCL Hausa ranar Alhamis, dan majalisar ya ce shekarunsa sun kai ya san abin da ya fi dacewa da shi kuma ya yankewa kansa hukunci kan abin da fi dacewa da shi. Kofa ya ce, “Ita kanta jam’iyyar ta...
A yanzu haka yankuna da dama wadanda a baya ba su fuskanci kalubalen matsalar tsaro ba, a yanzu haka sun fara dandana ukubar ta’addanci da bakuntar sansanin ‘yan gudun hijira. Kalubalen tabarbarewar tsaro da kiran da shugaban rundunar tsaro ta Kasa, Janar Christopher Musa ya yi kan ‘yan Nijeriya su dauki matakan kare kai ya haifar da cece- kuce musamman ga galibin jama’a da ke ganin gwamnati ta kasa. Da yawan jama’a na ganin duk da makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro da kwarewar jami’an sojoji amma ‘yan ta’adda sun rinjaye su har suna ikirarin jama’a su dauki matakan kare kai. Janar Musa wanda daga baya ya janye kalamansa, tun da farko ya bukaci ‘yan Nijeriya da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i da sauran jagororin jam’iyyar ADC kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye. A cewar takardar wacce Aminiya ta gani, an gayyace su ne domin su yi wa rundunar bayani kan zargin su da hadin baki da tunzura jama’a wajen tayar da tarzoma da kawo wa zaman lafiya tarnaki a jihar. An naɗa Benjamin Hundeyin sabon kakakin ’yan sandan Nijeriya Cin amana shi ne tsarin siyasa a Najeriya — Jonathan Takardar, wacce ke dauke da kwanan watan hudu ga watan Satumban 2025 dai na dauke ne da sa hannun Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (SCID), Uzairu Abdullahi. Takardar ta ce, “Wannan sashen namu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da ake gudanar da bukukuwan Mauludi a sassa daban-daban a garuruwan Najeriya, wasu yankunan na gudanar da nasu bukukuwar na daban. Ko yaya ake gudanar da bikin Sallar Gani? NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda ake gudanar da bikin sallar a wasu garuruwan kasar Hausa. Domin sauke shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce siyasar Nijeriya ta ginu ne a kan cin amana, la’akari da irin cin amanar da ya ce ya fuskanta matuƙa a lokacin da yake neman tazarce a Zaben 2015. Jonathan ya bayyana haka ne a wurin bikin cika shekara 70 na tsohon abokinsa, Cif Mike Aiyegbeni Oghiadomhe, da aka gudanar a Benin, babban birnin Jihar Edo, a ranar Alhamis. An naɗa Benjamin Hundeyin sabon kakakin ’yan sandan Nijeriya Ɓarkewar cutar Ebola ta kashe mutum 15 a Congo Ya ce daga cikin abubuwan da ya fahimta a siyasar Najeriya shi ne wahalar samun ɗan siyasa mai gaskiya da tsayawa a kan kalamansa. A cewarsa, galibin ’yan siyasar Nijeriya ba su da riƙon gaskiya ko...
Sai dai soja ɗaya ya samu rauni kaɗan amma yana cikin koshin lafiya. Haka kuma sun lalata tayoyi guda huɗu na mota, sannan manyan motoci biyu sub kama da wuta a yayin arangamar. Laftanal Kanal Uba ya ƙara da cewa sojojin na ci gaba da gudanar da ayyuka a yankin domin hana ‘yan ta’adda damar kai hari tare da tabbatar da kayan agaji sun isa Damasak lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ranar 3 ga watan Satumbar shekarar nan ta 2025, babbar rana ce da ta cancanci a tuna da ita, inda kasar Sin ta gudanar da gagarumin bikin faretin soja a Beijing, don tunawa da tarihi, da jarumai da ’yan mazan jiya, da nuna kishin zaman lafiya, tare da kirkiro kyakkyawar makoma. A gun bikin maraba da baki da suka shigo Beijing don halartar bikin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar kasar Sin suka yi da mamayar dakarun Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya da aka yi ranar 3 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, tarihin ya nuna mana cewa, ba za a iya girgiza imanin dan Adam ga neman adalci...
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya amince da naɗin CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon Kakakin ’Yan Sanda na Ƙasa (FPRO). Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar. Ɓarkewar cutar Ebola ta kashe mutum 15 a Congo Saudiyya ta ƙaƙaba wa masu laifukan rashin ɗa’a sabuwar tara Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasance kakakin rundunar ’yan sanda reshen Jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana wannan aiki. Hundeyin ya yi karatu a fannin Turanci da kuma nazari da halayyar masu laifi da tsaro wato Criminology da Security Psychology. Haka kuma, memba ne na ƙungiyoyin ƙwararru kamar Nigerian Institute of Public Relations (NIPR) da International Public...
Dakarun soji na rundunar ‘yantar da al’ummmar kasar Sin ko PLA reshen kudanci, sun gudanar da jerin sintiri a yankin tekun kudancin kasar Sin. A cewar kakakin rundunar Tian Junli, sojojin sun gudanar da ayyukan sintirin ne a jiya Laraba kamar yadda suka saba yi lokaci bayan lokaci. Tian Junli, ya ce kasar Philippines ta yi hadin gwiwa da wasu kasashe na wajen yankin, wajen tsara abun da suka kira sintirin hadin kai, wanda hakan ya illata yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Tian, ya jaddada cewa sojojin rundunar PLA reshen kudanci, suna cikin matukar shirin kare ikon mulkin kai na yankunan Sin, da ma hakkokin teku na kasar. Ya ce “Duk wani yunkuri na tayar da husuma a...
Ya kuma nuna damuwa kan rikicin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankali a jihar. Game da tsaro kuwa, Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin da ke tasowa a wasu sassan jihar. Ya ce sun ƙarfafa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da shugabannin matasa, sannan an ƙara tsaurara matakan tsaro a iyakokin jihar domin hana miyagu shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Har ila yau, a dai yau din shugaba Xi ya gana da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar juyin juya halin jama’ar kasar Laos kuma shugaban kasar Thongloun Sisoulith, da shugaban kasar Vietnam Luong Cuong, da shugaban kasar Cuba Miguel Diaz-Canel, da firayin ministan jamhuriyar Slovakia Robert Fico, da shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic a nan birnin Beijing. (Mai fassara: Jamila) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Kim Jong Un, babban sakataren jam’iyyar ma’aikata ta kasar Koriya ta Arewa, kuma shugaban harkokin gudanarwa na kasar Koriya ta Arewa, a yau Alhamis a birnin Beijing. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’in siyasar kungiyar Hamas ya mayar da martani ga shugaban kasar Amurka Trump cewa: Netanyahu yana son yaki mara iyaka ne Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas Izzat al-Rishq ya fada a yammacin jiya Laraba, yayin da yake mayar da martani ga bukatar shugaban Amurka Donald Trump na sakin dukkan fursunonin Isra’ila, cewa “Hamas ta amince a ranar 18 ga watan Agusta kan shawarar masu shiga tsakani, wadda ta dogara ne kan shawarar Witkoff, kuma har yanzu Netanyahu bai bayyana matsayinsa ba.” A martanin da ya gabatar kan furucin Trump, al-Rishq ya tabbatar da cewa, kungiyar Hamas ta bayyana shirinta na cimma cikakkiyar yarjejeniya, inda za a saki dukkan fursunonin, a madadin adadin da aka amince na fursunonin Falasdinu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Matasan Ƙaramar hukumar Shagari sun kashe wasu ’yan bindiga shidda da ake zargin suna cikin waɗanda suka addabi yankin Ƙaramar hukumar Shagari a Jihar Sakkwato. Wani matashi ya yi wa wakilinmu bayanin yadda lamarin ya faru ya ce, ’yan bindigar sun zo kan Jakuna a cikin dajin da ba kowa, a safiyar Alhamis inda mutane da ke tsare gari ba su watse ba suka gansu a nan ne suka yi masu ƙofar raggo, suna tare da shanun da suka sata da wasu baƙin shanu. Mai taɓin hankali ta haihu a tsakiyar kasuwa a Oyo Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 60 a Neja “An gansu su bakwai an kashe shidda daga cikinsu an bar guda raye aka...
Matasan Ƙaramar hukumar Shagari sun kashe wasu ’yan bindiga shidda da ake zargin suna cikin waɗanda suka addabi yankin Ƙaramar hukumar Shagari a Jihar Sakkwato. Wani matashi ya yi wa wakilinmu bayanin yadda lamarin ya faru ya ce, ’yan bindigar sun zo kan Jakuna a cikin dajin da ba kowa, a safiyar Alhamis inda mutane da ke tsare gari ba su watse ba suka gansu a nan ne suka yi masu ƙofar raggo, suna tare da shanun da suka sata da wasu baƙin shanu. Mai taɓin hankali ta haihu a tsakiyar kasuwa a Oyo Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 60 a Neja “An gansu su bakwai an kashe shidda daga cikinsu an bar guda raye aka...
A gefe guda kuma, gwamnatin China ta ba da tallafin dala miliyan ɗaya ($1m) domin taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa a Arewacin Nijeriya. Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziƙi, Abubakar Bagudu, ya ce za a yi amfani da kuɗin yadda ya dace, yayin da Jakadan China a Nijeriya, Yu Dunhai, ya nuna goyon baya da jajensa ga mutanen da abin ya shafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Adadin mutanen da suka rasu a hatsarin jirgin ruwa da ya auku a yankin Malale, da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, ya kai 60. Jirgin ruwan, wanda ya ɗauko kusan mutum 90, ya tashi daga Tugan Sule a gundumar Shagunu, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Dugga. ‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’ Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda Mutanen da ke cikin sun tafi yin gaisuwar ta’aziyya ne, lokacin da hatsarin ya auku a ranar Talata, 2 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 11:30 na safe. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA),...
Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da ɓullar cutar cholera a garin Tureta, ƙaramar hukumar Tureta, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin. Kwamishinan lafiya na jihar ya ce an tura samfurin majinyatan zuwa ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa da ke Jihar Oyo domin tabbatar da cutar. Ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da magunguna ƙyauta tare da taimakon likitoci, inda ya bayyana cewa da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa suna amsawa da magani. Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto Sai dai, mazauna yankin sun yi iƙirarin cewa aƙalla mutane goma ne ke mutuwa...
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya 14 daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba. Cibiyar Gargaɗi Kan Ambaliya (FEWS) ta ma’aikatar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis. Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin Sambisa Sanarwar, wacce Daraktan Kula da Zaizayar Ƙasa da Ambaliya na ma’aikatar ya fitar, ta gargadi dukkan masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye domin kare kansu. A cewar sanarwar, garuruwan da jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da Ebonyi (Afikpo), Kuros...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kashe ’yan ta’adda sama da 15 a wani harin jiragen yaƙi da aka kai dajin Sambisa, da ke Jihar Borno. Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya ce an ƙaddamar da harin ne a ranar Laraba karkashin Operation Haɗin Kai. Umar FK ya fice daga PDP zuwa APC da magoya bayansa a Gombe Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa Ya ce sun samu bayanan sirri da suka nuna cewa mayaƙan da ke da hannu a hare-haren a yankin Bitta sun ɓuya a wajen. Ya ce hare-haren sun lalata maɓoyar ’yan ta’addan tare da raunata da dama da cikinsu. Ejodame ya ƙara da cewa wannan ya nuna ƙwarewar NAF da kuma...
Siyasar Jihar Gombe ta ƙara ɗaukar zafi yayin da fitaccen ɗan siyasar nan, Umar Faruk FK, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dimbin magoya bayansa, tare da komawa APC. FK, ya bayyana cewa PDP ta gaza bayar da shugabanci nagari a jihar, shi ya sa ya yanke shawarar barin ta. 2027: ’Yan adawa na ƙoƙarin sanya APC fara kamfe da wuri — Tinubu Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa Ya ce ya mara wa Gwamna Inuwa Yahaya baya bisa ayyukan ci gaba da ya ke gudanarwa. “Marar kishin Gombe ne kawai ba zai ga nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ke samu ba,” in ji Umar FK. Ya ƙara da cewa shi da magoya bayansa za su mara...

Araqchi: Iran ba ta fargabar shiga tattaunawa kuma ba ta tsoron kare kanta idan aka kallafa mata yaki
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce Iran ba ta fargabar shiga sabuwar tattaunawa don warware duk wasu batutuwan da ba su dace ba, amma ba ta fargabar fuskantar wani sabon yakin da makiya za su iya sanyawa kasar. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba bayan da ya raka shugaba Pezeshkian a ziyarar da ya kai kasar Sin. “Ba mu da tsoron tattaunawa, kamar yadda ba mu da tsoron yaki,” in ji shi. Wannan furuci ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin Amurka da sha’awar shiga sabuwar tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Tehran ba ta yi watsi da yiwuwar shiga sabon tsarin diflomasiyya...
TotalEnergies da takwararta ta South Atlantic Petroleum sun rattaba hannu kan yarjejeniyar (PSC) don lasisin binciken PPL 2000 da PPL 2001 a gabar tekun Najeriya, wadanda aka ba su sakamakon zagayen binciken 2024 da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ta shirya. A cewar sanarwar ta TotalEnergies, PPL 2000 & 2001, wanda ke da fadin kasa kimani kilomita murabba’i 2,000, yana cikin kogin yammacin Delta. Ya kara da cewa shirin aikin ya hada da hako rijiyar bincike daya. “An karrama TotalEnergies da zama kamfani na farko na kasa da kasa da aka ba da lasisin binciken bincike a Najeriya a cikin sama da shekaru goma, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a cikin dogon lokaci tare da...
Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya damuwa da maganganun ‘yan siyasar Arewa da ke ayyana niyyar ƙalubalantar shi a zaɓen 2027, duba da yadda yankin Arewa ya kasa dunkulewa wuri guda. Jibrin, wanda ke wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji ta jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka a shirin Politics Today na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Laraba. Ya ce, “Abin da muka saba yi shi ne, idan wani ya taso daga Arewa, sai mu haɗu mu rusa shi. Wannan shi ake yi. Kuma ina tabbatar maka, waɗanda suke cewa za su tsaya takara su kayar da Bola Tinubu, shi kuwa yana murna ne saboda yana ganin yadda muke cikin rikici da rarrabuwar...
Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital na Najeriya, Mista Bosun Tijani, ya yi jawabi ga shugabannin kasashen duniya kan makomar dijital ta Afirka a GITEX NIGERIA Government Leadership & AI Summit a Abuja. Taron dai ya fara bugu na farko na GITEX NIGERIA kafin daga bisani ya koma Legas a ranakun 2-3 ga watan Satumba. Wanda aka gudanar a karkashin jagorancin shugaban Najeriya Bola Tinubu, GITEX Nigeria na samun goyon bayan ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani tare da hadin gwiwar hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA). Gwamnatin Jihar Legas ce ta amince da taron, kuma KAOUN International, mai shirya taron GITEX na duniya ne ta shirya shi. A cikin bayyanarsa na farko a bainar jama’a...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya zargi jam’iyyun adawa da jan APC cikin harkokin siyasa kafin lokacin zaɓen 2027. Sai dai ya ce ba zai bari hakan ya karkatar da hankalinsa daga shugabantar Najeriya ba. NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 Za a koma rubuta jarabawar WAEC a komfuta Yayin da yake ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas a Abuja, Tinubu ya yaba da ƙoƙrinsu wajen yaƙi da rashin tsaro tare da alƙawarin yin aiki da su kan batun ’yan sandan jihohi da kuma ayyukan gina hanyoyi. “A siyasa, ’yan adawa suna ƙoƙarin janyo mu mu fara kamfen da wuri. Amma duk da haka, ba zan bari a karkatar da hankalina ba. Na mayar da hankali...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027. A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko kadarorin jam’iyyu ko ma daidaikun ’yan siyasa. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Da Mutane Zasu Bi Wajen Neman Diyya DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda siyasar 2027 za ta kasance duba da yadda hali yake a yanzu. Domin sauke shirin, latsa nan
A ranar 20 ga watan Yulin bana, an gano gawarwaki 85 a gefen buhunan abinci masu dauke da tambarin MDD, wadanda suka hada da mata da yara. Wasu na ci gaba da rike buhunan abinci lokacin da aka same su, yayin da wasu yaran ke cikin yanayi na nuna galabaita kafin mutuwarsu. Wannan shi ne mummunan sakamakon harin sama da Isra’ila ta kai a wani wurin rarraba kayan agaji a zirin Gaza. Abun takaici shi ne, ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan abun ba. Wani rahoton MDD ya nuna cewa, mutum guda na mutuwa a duk minti uku a fagen yaki a fadin duniya. Mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon yaki, su ne mafi daukar hankali...
Nakore, memba ne na ƙungiyar Injiniyoyin Nijeriya (NSE), kuma ya taɓa rike muƙamin Sakataren Zartarwa na Hukumar Wutar Lantarki a karkara a Jihar Jigawa. Farfesa Kodage kuwa, kwararre ne a fannin ilimi da yake da gogewa a harkar koyarwa da al’amuran gudanarwa. Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati take yi domin ƙarfafa shugabanci a tsarin ilimi da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin tafiyar da sababbin jami’o’in da aka ɗaukaka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wata matashiya mai shekara 20, Maryam Atiku, bisa zargin binne jaririyar da ta haifa da ranta a unguwar Nasarawa da ke Kamba a Karamar Hukumar Dandi. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, CSP Nafi’u Abubakar, ya fitar a wannan Larabar. Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 29 a Neja Dalilin da Najeriya ba ta jin tsoron matakan Trump — Tinubu Ya ce matashiyar bayan ta haifi jaririyar, ta naɗe ta a cikin wasu zannuwan atamfa guda uku, sannan ta kai ta wani daji da ake kira Malam Yaro a yankin Nasarawa, inda ta tono rami ta binne ta da ranta. Sai dai a cewar...

Firaministan Senegal: Yadda Sinawa Ke Girmama Tarihi Da Kiyaye Labarun Abubuwan Da Suka Faru Da Su Na Da Matukar Burgewa
Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi. Sonko ya ce, duk kasar da ba ta iya tuna abubuwan da suka faru da ita a tarihi za ta yi matukar wahala ta dauki darasi daga abin da ya gabata, kuma tana iya saurin maimaita kura-kurai da kuma shan wuyar tashin hankalin da aka shiga a tarihi. Abin da ya yi matukar ba shi mamaki shi ne yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye labarun abubuwan...
Aƙalla mutum 29 sun rasu a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a gabar kogin Malale da ke cikin Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa, kwale-kwalen wanda ke ɗauke da fasinjoji 90, ya tashi ne daga Tugan Sule da ke yankin Shagunu, inda ya nufi Dugga domin zuwa wata ta’aziyya. Dalilin da Najeriya ba ta jin tsoron matakan Trump — Tinubu Boko Haram ba kiristoci kaɗai suke kashewa a Arewa Maso Gabas ba — Ndume Majiyoyi sun bayyana cewa cikin waɗanda suka mutu har da mata da ƙananan yara, kuma zuwa yanzu an gano gawarwaki 29, yayin da aka ceto mutum 50 da ransu, sai kuma wasu mutum biyu da har yanzu ake ta ƙoƙarin lalubo...
“A madadin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ina kara tabbatar da tsayin dakar Nijeriya ga manufofin GGC. Babu wanda zai iya gurgunta rawar da hukumar ke takawa wajen samar da hadin kai, zaman lafiya, da ci gaba mai dorewa a mashigin tekun Guinea,” in ji shi. Ya yaba wa mahukuntan GGC, yana mai ba su tabbacin cewa, “Nijeriya na nan tsayin daka kan kare manufofin hukumar.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya ce ba daidai ba ne a riƙa cewa Boko Haram Kiristoci kawai suke kashewa a Arewa maso Gabas. Ya bayyana cewa ƙungiyar tana kai wa Musulmi da Kiristoci hare-hare baki ɗaya, don haka bai kamata a alaƙanta ta da addini ɗaya ba. Kotu ta ɗaure wani mutum kan kashe saurayin ’yarsa a Ekiti An ƙone ‘ɓarawon’ babur ƙurmus a Binuwai Ndume, ya mayar da martani ne kan wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai ta wallafa wanda ta yi iƙirarin cewa dukkanin waɗanda aka kashe kwanan nan a hare-haren Boko Haram Kiristoci ne. Ya ce a hare-haren da suka faru a ƙarshen mako a Jihar Borno, Musulmi biyar aka kashe...
Kazalika, wannan biki na tunawa da nasarar fatattakar zalunci yana tunatar da mu mahimmancin waiwaye a kan tarihi. Fina-finai da aka yi game da hakan kamar “Dead to Rights”, da bikin nune-nunen a sassan yankin Macao, da faretin soja a birnin Beijing, hidindimu ne na sake duba tarihi, da sadaukarwar al’ummomin da suka gabata domin ci gaba da zaburar da na yanzu da wadanda za su zo gaba. Birnin Beijing ya cika da annashuwa da alfahari yayin da dandalin Tian’anmen ya shaida gagarumin faretin soji domin bikin na yau. An yi gaisuwar ban-girma ta hanyar harba bindigogi 80 a sassan babban birnin domin karrama mazan jiya da suka kwanta dama da kuma wadanda suke raye. Sojoji sun yi tattaki cikin...
Tarihin yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya ya nuna mana wasu tunani masu zurfi, wadanda jama’ar kasar Sin suka san su sosai: Da farko dai, komai wahalhalun da aka sha, adalci zai yi galaba a kan muguntawa, haske kuma zai kori duhu. Wannan tamkar doka ce ta tarihi. Na biyu, ‘yan Adam na da makomar bai daya. Ya kamata a samu daidaituwa, da jituwa, da cude-ni-in-cude-ka, tsakanin kasashe da kabilu daban daban, ta yadda za a samu damar tabbatar da tsaron bai daya, da kawar da yaki daga karshensa. A zamanin da muke ciki, ana ta samun abkuwar rikice-rikice a duniya, inda dan Adam suka sake fuskantar bukatar...
Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya ce ba daidai ba ne a riƙa cewa Boko Haram Kiristoci kawai suke kashewa a Arewa maso Gabas. Ya bayyana cewa ƙungiyar tana kai wa Musulmi da Kiristoci hare-hare baki ɗaya, don haka bai kamata a alaƙanta ta da addini ɗaya ba. Kotu ta ɗaure wani mutum kan kashe saurayin ’yarsa a Ekiti An ƙone ‘ɓarawon’ babur ƙurmus a Binuwai Ndume, ya mayar da martani ne kan wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai ta wallafa wanda ta yi iƙirarin cewa dukkanin waɗanda aka kashe kwanan nan a hare-haren Boko Haram Kiristoci ne. Ya ce a hare-haren da suka faru a ƙarshen mako a Jihar Borno, Musulmi biyar aka kashe...
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce da a ce yana da cikakken iko da jami’an tsaro, da zai iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar shi a cikin mako biyu. Gwamnan ya kuma ce ya san dukkan inda ’yan bindigar jihar suke buya. Da yake jawabi a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, gwamnan ya ce babban kalubalen shi a yaki da ’yan bindiga a jihar shi ne rashin cikakken iko da jami’an tsaro. ya ce shugabannin rundunonin tsaron da ke jihar suna karbar umarni ne kawai daga hedkwatocinsu da ke Abuja, bad aga wajen shi ba. A cewar Gwamnan, “Na rantse da Allah na san duk inda wani shugaban ’yan bindiga yake a Zamfara,...

Ƙungiyar masu kafafen yada labarai na Arewa za ta daukaka kara kan hukuncin kotu a kan tashar Arewa24
Ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya (NBMOA) ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na yin watsi da ƙarar da ta shigar a kan tashar Arewa24, inda ta ce za ta ɗaukaka ƙara. Idan za a iya tunawa, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a watan Agusta, ta yi watsi da karar da kungiyar NBMOA ta shigar a kan Arewa24, saboda “rashin hukunci da rashin cancanta”, kamar yadda aka gani a cikin kwafin takardar hukuncin kotun (CTC). Kotun, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar da cewa AREWA24 tana gudanar da harkokinta ne bisa ƙa’ida, kuma ba ta da hurumin samun ƙarin lasisin gudanar da ayyukanta, ba tare da karya wata doka...
Domin ya ce wannnan matsala ce da ta shafi ƙasa, kuma ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin sanin halin da ƙasar ke ciki. A cewarsa wannan babban zargi ne, don haka bai kamata a manta da shi ta hanyar yin jawabi ba tare da wasu gamsassun hujjoji ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata. Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Wata kungiya mai rajin tabbatar da zaman lafiya a jihar mai suna Katsina Security Community Initiative ce ta shirya taron na ranar Talata da nufin lalubo bakin zaren kan matsalar tsaron da ta addabi jihar. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi Tinubu ya dawo da shugaban NTA da ya sauke Katsina dai ta shafe tsawon shekaru tana...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a rungumi akidun tabbatar da daidaito da adalci, tare da tsayawa tsayin daka kan tafarkin samar da ci gaba cikin lumana, da kara azamar inganta rayuwar al’umma a ko da yaushe. Shugaba Xi ya yi kiran ne a yau Laraba, yayin bikin taron tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Xi ya ce, shekaru 80 da suka shude, bayan shafe shekaru 14 ana gwabza kazamin yaki, al’ummar Sinawa sun yi nasarar murkushe dakarun mamaya na kasar Japan, tare da ayyana cimma cikakkiyar nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Wannan muhimmiyar gaba...
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, biyar ga watan Satumban 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Ana dai yin bikin ranar ce dai da ake kira ta Mauludi a duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wat ana uku a shekarar Musulunci. DAGA LARABA: Yadda Mata Dake Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, ranar Laraba a madadin gwamnatin, kamar yadda Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani ta sanar. Ministan ya kuma taya ’yan Najeriya murna, inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayen Annabin na zaman lafiya, kaunar jama’a, hakuri, tawali’u...
Hukumar kula da madatsun ruwa ta Nijeriya (NiHSA), ta gargaɗi cewa wasu jihohi a Arewa cewar za su iya fuskantar ambaliya a makonni biyu na farkon watan Satumba. A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar ta ce gaba ɗaya jihohi 29 da Babban Birnin Tarayya Abuja ne ke cikin barazanar ambaliya daga 1 zuwa 15 ga watan Satumba. Sabuwar Ajandar Mulkin Duniya Ta Nuna Alhakin Da Kasar Sin Ta Dauka Shugaban Uganda: Jarin Sin Na Taimakawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Kasashen Afirka Hukumar ta ce ambaliyar za ta iya shafar ƙananan hukumomi 107, garuruwa 631, da kuma tituna 50 a sassa daban-daban. Jihohin da suka fi shiga hatsari sun haɗa da: Borno, Zamfara, Jigawa, Kebbi, Yobe, Filato,...

Xi Jinping Ya Duba Faretin Rundunonin Sojoji Da Kayayyakin Soja, Shugabannin Kasashe 26 Su Ma Sun Halarci Bikin
Shekaru 80 da suka gabata, al’ummar kasar Sin sun samu gagarumar nasara a yakin kin hare-haren sojojin Japan bayan shekaru 14 masu cike da wahalhalu, tare da bayyana cikakkiyar nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. Sin ta fara yakin kin hare-haren ne tun daga farko har karshe a tsawon lokaci, kuma bisa gagarumar sadaukarwar al’ummun Sin, kasar ta bayar da goyon baya a babban fagen yaki na yaki da mulkin danniya a gabashin duniya, tare da ba da muhimmiyar gudummawa ga samun nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. (Amina Xu, Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Tarihi ya yi mana gargadi da cewa, makomar dan adam tana hade da juna, kuma kowace kasa, da kowace kabila dole ne su daidaita da juna, su zauna lafiya, su taimaki juna, domin ta haka ne kawai za a iya kiyaye tsaro na gama gari, da kawar da tushen yaki, da tabbatar da tarihi bai maimaita kansa ba! A jawabin nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, al’ummar kasar Sin babbar al’umma ce mai dogaro da kanta, wadda ba ta jin tsoron masu nuna karfin tuwo. A lokutan baya, an sha fama da gwagwarmaya tsakanin adalci da mugunta, tsakanin haske da duhu, tsakanin ci gaba da koma baya, kuma jama’ar kasar Sin sun hada kai sun tashi tsaye wajen yaki da...
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar Habasha, domin gina daya daga cikin manyan masana’antun takin zamani a duniya a garin Gode. An rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin rukunin Dangote da kamfanin zuba jari na Habasha (EIH), wanda zai baiwa rukunin Dangote damar rike hannun jarin kashi 60 cikin dari, yayin da EIH zai rike kashi 40 cikin dari. Ana has ashen cewa idan an kammala aikin, zai kasance cikin manyan masana’antun samar da takin zamani guda biyar na duniya, wanda zai rika samar da takin zamani ton miliyan uku a kowace shekara. A cewar EIH, za a kammala aikin a cikin...
Jami’an Iran sun yaba matuka da irin nasarorin da aka samu a yayin halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian a taron kungiyar Shanghai (SCO) a kasar China. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran ta yi amfani da tsarin diflomasiyya a bangarori daban-daban a yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekara-shekara a kasar Sin. Gharibabadi ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon shafin Twitter a jiya Talata, inda ya yi bayani kan abubuwan da suka shafi taron, wanda shugaba Masoud Pezeshkian, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin ya aiwatar da su. A cewar jami’in diflomasiyyar, halartar babban jami’in gudanarwa na kasar Iran a taron ya...
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar rayukan da za su kai sama da miliyan 100, wadanda daga cikinsu sojoji da fararen hula miliyan 35 ne Sin ta yi asara. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan mummunar akida ta mulkin danniya, yayin da ta shiga cikin sahun sojojin sauran kasashe a yakin duniya na biyu. Kafada da kafada suka yi gumurzu wajen murkushe maharan kasashen Japan, Jamus da...
Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya suka samu a yakin duniya na biyu. Bugu da kari, Guterres ya jaddada ta hanyar nuna batutuwan tarihi cewa, babbar mamayar da Japan ta yi wa Sin ita ce farkon yakin duniya na biyu na gaskiya. Guterres ya yi imanin cewa, tsayin daka da kasar Sin ta yi wajen yin tir da hare-haren Japan, ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru da dama, tare...
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku. ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027. A ’yan kwanakin nan ne aka...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce alakar Sin da Rasha ta zama misali na kyakkyawar dangantaka tsakanin manyan kasashe, wadda ke kunshe da ingantaccen yanayin kawance na makwafta, da cikakken salon tafiya tare bisa manyan tsare-tsare, da hadin gwiwar cimma moriyar juna. Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin zantawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Beijing. A nasa tsokacin kuwa, shugaba Putin ya ce shawarar da shugaba Xi ya gabatar game da tsarin shugabancin duniya ta zo a lokacin da ake matukar bukatarta, kuma wajibi ne a yi aiki da ita, kana za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance gibin dake akwai a tsarin shugabancin duniya. Ya ce a nata bangare, Rasha a...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hakimin Bagaji Odo a Karamar Hukumar Omala ta Jihar Kogi, David Wada. Rahotanni sun ce basaraken ya faɗa tarkon ’yan bindigar ne a ƙauyen Ojuwo Ugweche da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, yayin da yake dawowa daga taron sarakunan gargajiya a Abejukolo, hedikwatar ƙaramar hukumar. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Wani mazaunin yankin, Maji Ahiaba, ya bayyana cewa a ’yan kwanakin nan ƙauyen Ojuwo Ugweche na fuskantar hare-haren masu ta’adar garkuwa da mutane, duk da cewa a baya an taɓa tura jami’an tsaro da ’yan sa-kai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata. Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da kuma jagorancin cike gibin kudi na samar da ci gaba da bunkasa. Sabuwar ajandar mulkin duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta yi magana kai tsaye kan wasu muhimman abubuwa guda uku a tsarin jagorancin duniya, wato rashin daidaiton iko, da rarrabuwar ra’ayoyi, da kuma rashin daukar matakai. Ajandar, wadda ta fitar da wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar wa auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24 Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya karu zuwa shahidai 63,633, tare da jikkatan wasu 160,914. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar alkalumman baya-bayan nan da ma’aikatar ta...
Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya. A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce za a karrama Sarkin tare da wasu fitattun ’yan Najeriya guda shida a babban taron shekara-shekara da cibiyar ke shiryawa. Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025, a Cibiyar Karatun Alƙur’ani...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci Golan zai riƙa amfani da riga mai lamba 99 domin ranar haihuwarsa ta 1999, kamar yadda ƙungiyar ta sanar. A jawabin da ya yi dangane da komawa ƙungiyar, Donnarumma ya ce yana cike da farin ciki da jin daɗi. “Na koma ƙungiya da ke cike da zaratan ’yan wasa, sannan kuma ƙungiya...
Hukumar NDLEA a Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na ɗauke da ƙwayoyi, tare da tabar wiwi guda 48. An cafke wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, bayan an gano kayan a cikin tirela ɗauke da kekuna a kan hanyar Zariya zuwa Kano a Gadar Tamburawa. ’Yansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Katsina, Sun Ƙwato Makamai ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Daba 107 A Kano, Sun Ƙwato Makamai Da Ƙwayoyi NDLEA ta ce tana tsare da wanda ake zargin da kuma kayayyakin, yayin da ake ci gaba da bincike. Hukumar ta buƙaci jama’a su riƙa sanar da ita duk wani abin da suka zarga na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi. Daga kanmu, magana ta...
Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako. A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da suke aiki a gonakinsu. Haka zalika, a yankin Mussa da ke Askira/Uba, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen a ranar asabar da daddare, inda suka kashe matasa uku, kafin su ƙona wasu gidaje da shaguna da ƙauyen. Waɗannan munanan hare-haren sun jefa al’ummomin cikin zaman makoki wanda ya ƙara nuna damuwa kan rashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin. Sai dai kuma Sanata Ndume...
Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Abdulwahid Muhammad Nour na kungiyar ‘The Sudan Libration Movementa’ Wato (SLM) wacce take iko da yankin yana fadar haka. Ya kuma kare da cewa, zaizeyar kasa ta aukune bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin. Ya kuma kammala da cewa mutum guda ne kacal ya tsira da ransa a garin Marra dake kan tsaunin. Kungiyar ta bukaci taimakon MDD da kuma sauran kungiyoyin Agaji a duniya don fidda gawakin mutanen da zaizayar kassar ta bisne a kan tsaurin. Kasar Sudan dai tana cikin yaki fiye da shekaru...
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), ta yi kira ga Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) da ta ƙara mayar da hankali wajen yada labarai kan wasannin gargajiya, irin su langa da kokawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe wanda shi ne shugaban ALGON reshen Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin SWAN na jihar suka kai masa ziyarar ban girma, inda suka nemi goyon bayansa kan babban taron bita da ƙungiyar ke shirin gudanarwa. A cewarsa, ƙara bayar da muhimmanci ga wasannin gargajiya zai taimaka wajen jan hankalin matasa zuwa harkokin ci-gaban rayuwa, tare da rage yawan fadawa cikin laifuka da shan miyagun ƙwayoyi. Ya kuma shawarci SWAN da ta ƙulla alaƙa...
’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai a jami’ar mai suna Jon Reider, ya musanta iƙirarin na Kemi Badenoch, wadda ta yi kaurin suna wajen sukar ƙasarta ta haihuwa. Kemi Badenoch ta yi iƙirari cewa ta samu gurbin ƙaramin tallafin kuɗi daga Jami’ar Stanford, amma rashin kuɗin iyayenta ya hana ta amfani da damar. Sai dai Jon Reider, wanda a lokacin yake kula da ɗalibai daga ƙasashen waje da tallafin karatu a Stanford,...
An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta. Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen a jiya, inda aka gabatar da jawabai daban-daban, da ke kara tabbatar da aniyar al’ummar kasar Yemen wajen ci gaba da bin tafarkin wadanda suka yi shahada, domin mara baya ga al’ummar Gaza mara kariya. A nasa bangaren Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan wannan hari na wuce gona da...
shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na nukiliya a gabar tekun Venezuela. Inda Ya kira wannan matakin da cewa shi ne mafi muni da Amurka ta dauka a tsawon shkaru a yankin Caribbean. Maduro ya zargi Washington da aiwatar da manufar matsin lamba ta soja a kan Caracas, wanda ya tilasta wa Venezuela ayyana cikakken shirin tsaron kasa. “Venezuela kasa ce mai zaman lafiya, amma al’ummarta mayaka ne kuma ba za su...
A lokacin wani taro da ya gudana tsakanin shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio gutteres a kasar china ya bayyana cewa iran tana da hakkin ta mallaki fasahar nukiliya na zaman lafiya, kana ya nuna damawarsa game da batun takunkumi da kasashen turai ke son sake kakabawa iran, Wannan bayanin na Gutteres ya kara fito da matsayin iran a mataki na kasa da kasa na hakkin mallakar fasahar nukiliya domin ayyukan zaman lafiya, a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tankiya tsakanin iran da kuma kasashin turai game da shirin ta na nukiliya da kuma yunkurin sanya mata takunkumai, A nasa bangaren shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya bayyana cewa...
Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari. Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa, Kodayake babu asarar rai. Bayan dawowar tsohon ministan a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gida ya yi zargin siyasa ce ta a da aka kai masa harin, yana mai jaddada cewa, harkar siyasarsa babu gudu babu ja da baya. “Shari’a ta tanadi ka kare kai, in aka kawo maka hari amma kai kar ka kai wa kowa hari, maganar siyasa ba gudu ba ja...
Kazalika, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin hada karfi da karfe wajen kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu, da samar da karin alfanu ga daukacin bil’adama ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ba da tabbacin cewa, Majalisar za ta kara sanya ido domin tabbatar da gaskiya da rikon amana ga yadda ake sarrafa kudaden jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp